Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United na turbar buga Champions League a badi
Manchester United ta ci Aston Villa 1-0 a wasan Premier League da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.
Minti na 39 da fara wasa United ta ci kwallo ta hannun Bruno Fernandes, wanda hakan ya ba ta maki uku a fafatawar.
Wannan nasarar da United ta yi a kan Aston Villa ta kawo karshen karawa 10 da kungiyar Villa Park ta yi a jere ba tare da an doke ta ba.
United mai kwantan wasa biyu tana ta hudu a kan teburin Premier da maki 63 da tazarar maki biyu tsakaninta da Newcastle ta uku mai maki 65.
Cikin 'yan hudun farko a teburin Premier League shine zai sa kungiyar ta wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai ta badi.
Ranar 4 ga watan Mayu, United za ta ziyarci Brighton domin buga Premier League.
Ita kuwa Wolverhampton za ta karbi bakuncin Aston Villa ranar 6 ga watan Mayu a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Manchester City mai kwantan wasa ta koma ta daya a kan teburin Premier, bayan da ta ci Fulham 2-1 ranar Lahadi.
Arsenal ta koma ta biyu da tazarar maki daya tsakaninta da City, ranar Talata Gunners za ta fafata da Chelsea a Emirates.