Arsenal da Chelsea na rububin Ivan, Graham Potter ka iya gadar Erik ten

Asalin hoton, getty images
Arsenal da Chelsea na sa ido kan dan wasan gaba na Brentford kuma dan asalin kasar Ingila, Ivan Toney, mai shekara 28 wanda farashinsa ka iya kai wa £40m.
Ejan din dan wasan gaba dan kasar Sweden, Viktor Gyokeres ya ce zai yi wa matashin mai shekara 25 ya ci gaba da zama a kulob din Sporting Lisbon idan har manajan nasa, Ruben Amorium wanda ake alakanta shi da Liverpool, ya bar kulob din.
Ana tsammanin tsohon kociyan Chelsea da Brighton, Graham Potter zai iya gadar manajan Manchester United, Erik ten Hag wanda aka rawaito cewa akwai yiwuwar ya fuskanci kora a wannan bazara.
Harwayau a wannan bazarar kulob din Chelsea na sa idon dan wasan gaba na Napoli kuma dan asalin Najeriya, Victor Osimhen mai shekara 25, to sai dai kulob din zai fi mayar da hankali ne kan sayar da 'yan wasa domin samun kudi.
Shi ma kociyan Chelsea din, Mauricio Pochettino da tawagarsa ba su gamsu da kokarin dan wasan kulob din na gaba kuma dan kasar Ukraine, Mykalo Mudryk, a wannan kakar wasannin.
Shi ma kulob din Bayer Leverkusen ya bi sahun Liverpool da Tottenham wajen rige-rigen cimma kwantaragi da dan wasan Leeds United na gege, Crysencio Summerville mai shekaru 22.
Shi ma kulob din Manchester United na zawarcin dan wasan AC Milan na gaba kuma dan asalin kasar Portugal, Rafael Leao mai shekaru 24 wanda aka kimanta cewa darajarsa ta kai fan miliyan 124.
Its kuwa Aston Villa na cike da fatan cimma dogon kwantaragi da dan wasanta na tsakiya dan asalin kasar Brazil mai shekaru 25, Douglas Luiz.
Manchester United za ta bar tawagar farko ta 'yan wasa 12 barin Old Trafford a wani yanayi mai kama da damar sake gina kulob din a wannan bazara.
Shi kuwa mai tsaron ragar nan dan kasar Jamus, Alexander Nubel mai shekaru 27 na shirin rattaba hannu kan kwantaragi da kulob din Bayern Munich wanda ya kunshi ci gaba da kwantaraginsa da Stuttgart har zuwa wata kakar wasannin.











