Me ya sa ba a ganin kyawun baƙaƙen ƴan mata?
Me ya sa ba a ganin kyawun baƙaƙen ƴan mata?
An wallafa
San Rechal mai tallar kayan ƙawa ce a birnin Puducherry na Indiya wadda ta ce tana fuskantar kyara da tsangwama saboda baƙar fatarta.
Amma wariyar da aka nuna mata ta sa mata ƙwarin gwiwar tunƙaho da baƙar fatarta.
A yau, matashiyar mai shekara 23 ta zama fitacciyar mai tallar kayan ƙawa.
Ta ce za ta ci gaba da magana a kan bambancin da ake nuna wa baƙaƙen ƴan mata.



