Real Madrid ta hada maki shida a wasa biyu a Champions League

Jude Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta je ta doke Napoli da cin 3-2 a wasa na bibiyu a cikin rukuni na uku a gasar Champions League ranar Talata.

Mai masaukin baki, Napoli ce ta fara cin kwallo a minti na 19 da fara tamaula ta hannun Leo Ostigard daga baya Vinicius Junior ya farke a minti takwas tsakani.

Saura minti shida su je hutu ne Ral Madrid ta kara na biyu ta hannun Jude Bellingham, haka suka je hutu kungiyar Sifaniya na cin 2-1.

Kenan Bellingham ya ci kwallo takwas da bayar da uku aka zura a raga tun komawarsa Real Madrid a bana, shi ne kan gaba a manyan gasar Turai biyar a wannan bajintar a matakin wanda ba a gurbin mai cin kwallaye yake buga tamaula ba.

Haka kuma kwallo na takwas ke nan da ya ci a Champions League jimilla, wanda bai kai shekara 21 da haihuwa ba, masu kwazon a baya sun hada da Erling Haaland yana mai kwallo 20 da Kylian Mbappe mai 19 a raga da Karim Benzema mai 12 da kuma Patrick Kluivert mai tara.

Daga baya ne Napoli ta farke ta hannun Piotr Zielinski a bugun fenariti, sai dai saura minti 12 a tashi, Napoli ta ci gida ta hannun Alex Meret.

Wasa na biyar kenan da aka fafata tsakanin Napoli da Real Madrid a gasar zakarun Turai.

Daya wasan na rukunin da aka buga ranar Talata a Jamus, Union Berlin, wadda karon farko da take buga gasar ta yi rashin nasara a gida da ci 3-2 a hannun Braga.

Ranar 23 ga watan Oktoba, Real Madrid za ta je gidan Braga, domin buga wasa na uku a rukuni na ukun.

Yayin da Union Berlin za ta karbi bakuncin Napoli a daya karawar ta uku-uku a cikin rukuni.