Messi zai koma Barca, Man United na son Suzuki, Arsenal na cinikin Zubimendi

Asalin hoton, INTER MIAMI
Chelsea ta kayyade farashin Christopher Nkunku, Arsenal na zawarcin Martin Zubimendi, Marcus Rashford yana son komawa Barcelona...
Chelsea za ta buƙaci fam miliyan 65 kan dan wasan gabanta Christopher Nkunku, mai shekara 27, a yayin da Bayern Munich ke zawarcinsa, inda rahotanni suka ce dan wasan na Faransa bai jin dadin zamansa a Stamford Bridge. (Athletic)
Arsenal na ci gaba da tattaunawa don siyan dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Spain Martin Zubimendi, mai shekara 25, a kan fan miliyan 51 a bazara. (Mail)
Marcus Rashford, mai shekara 27, zai fi son komawa Barcelona, maimakon sauran kungiyoyin da ke ta son yin zabarinsa a wannan watan idan ta tabbata lallai sai ya bar Manchester United. (Sports Spanish)
Juventus na gab da kulla yarjejeniyar aro don dauko dan wasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26. (Gazzetta dello Sport)
Liverpool ta ki amincewa da tayin fan miliyan 70 daga kulob din Al-Hilal na Saudi Arabiya kan dan wasan gaban Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25. (Anfield Watch)
West Ham na sha'awar sayen dan wasan gaban Portugal Andre Silva, mai shekara 29, a matsayin aro daga RB Leipzig na tsawon kakar wasa ta bana. (Guardian)
Aston Villa ta ki amincewa da tayin fan miliyan 40 daga West Ham kan dan wasan Colombia Jhon Duran mai shekaru 21. (Talksport)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Liverpool na zawarcin dan wasan gaba na Nurnberg Stefanos Tzimas, mai shekara 19, tare da yuwuwar samun dan wasan na Girka kan kudi kusan fan miliyan 20 sannan kuma yana jan hankalin Chelsea, da Brighton da Aston Villa. (Sky German)
Manchester United na daga cikin kungiyoyin da ke tunanin daukar golan Parma dan kasar Japan Zion Suzuki mai shekara 22, da aka sa wa farashin fam miliyan 40 (Talksport)
Kungiyar Flamengo ta Brazil na sha'awar daukar dan wasan tsakiya na Arsenal da Italiya Jorginho, mai shekara 33, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara (Sky Sports)
Dan wasan baya na Faransa Axel Disasi, mai shekara 26, shi ne dan wasa na baya-bayan nan da zai iya barin Chelsea saboda rashin samun lokacin buga wasa. (Mirror)
Celtic na daya daga cikin kungiyoyi da dama da ke son dauko dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Louie Barry, mai shekara 21, a matsayin aro, amma kungiyar ta Premier tana duba zabin da take da shi. (Sky Sports)
West Ham na tattaunawa da Marseille kan cinikin Elye Wahi dan Faransa mai shekara 22. (ESPN)
Dan wasan gaban Argentina Lionel Messi, mai shekara 37, zai iya komawa Barcelona a matsayin aro a lokacin hutun gasar Amurka da zarar ya kulla sabuwar yarjejeniya da Inter Miami. (El Nacional)
Tsohon dan wasan Manchester United da Spain Ander Herrera, mai shekara 35, na shirin komawa kungiyar Boca Juniors ta Argentina daga Athletic Bilbao ta La Liga. (Fabrizio Romano)











