Dalot zai ci gaba da taka leda a Man United shekara biyar

An wallafa

Diogo Dalot ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Manchester United zuwa kaka biyar.

An tsawaita kwantiragin dan wasan tawagar Portugal har zuwa karshen Yunin 2028 da cewar za a iya kara masa shekara daya.

Dalot mai shekara 24, ya koma Old Trafford daga Porto a 2018, wanda kawo yanzu ya buga wasa 107 a kungiyar.

Dalot ya yi wa United wasa 42 a dukkan karawa a kakar nan, wanda ya buga wa tawagar Portugal wasa 11.

Ya buga wasan karshe da United ta ci Newcastle kuma ta lashe League Cup a watan Fabrairu, kofin farko da United ta dauka tun 2017.

Haka kuma ya buga karawar daf da karshe da United ta yi nasara a kan Brighton a bugun fenariti a FA Cup.

Ranar Asabar United za ta kece raini da Manchester City a wasan karshe a Wembley, kofi na biyu da take fatan dauka a kakar farko karkashin Erik ten Hag.

United za ta buga Champions League a badi, bayan da ta kare a mataki na uku a kan teburin Premier League na bana da aka kammala, wanda City ta lashe.