Arsenal da Bayern na son Rice, PSG kuwa Silva

An wallafa

Arsenal na shirin taya Declan Rice na West Ham fam miliyan 92, kudin da Gunners din ba su taba kashewa ba a sayen dan wasa a tarihi. (The Telegraph)

Bayern Munich ma na sha'awar Rice domin kociyanta Thomas Tuchel na kokarin karfafa tsakiyar kungiyar. (Mirror)

Haka kuma kociyan Arsenal din Mikel Artetana son dan bayan Manchester City da Portugal Joao Cancelo, wanda yanzu yake zaman aro a Bayern Munich, amma kuma Arsenal din na ganin da wuya City ta yarda ta sayar mata da shi a bazaran nan mai zuwa. (Talksport)

Paris St-Germain na son Manchester City ta sayar mata da Bernardo Silva, bayan da cinikin dan wasan na tsakiya dan Portugal ya ki kayawa a bazarar da ta wuce, ana ganin farashinsa a yanzu zai kai kusan fam miliyan 70.(The Telegraph)

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp na son rike dan wasansa na tsakiya James Milner, dan Ingila mai shekara 37, wanda ke shirin barin kungiyar, domin ba shi aikin horad da 'yan wasa. (Mirror)

Manchester United ta cimma matsaya da dan bayan Napoli Kim Min-jae na Koriya ta Kudu . (Il Mattino daga Metro)

Dan wasan tsakiya na Arsenal da Norway Martin Odegaard na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar kasancewar kwantiraginsa na yanzu zai kare a 2025. (90min)

Kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso ya bayar da tabbacin ci gaba da zama a kungiyar ta Jamus a kaka ta gaba bayan da aka rika danganta tsohon dan wasan na Liverpool da aikin kociyan Tottenham da ba kowa a yanzu. (Sky Sports)

Dan wasan Arsenal Albert Sambi Lokonga, mai shekara 23, zai so tafiya Burnley domin sake hadewa da kociya Vincent Kompany, wanda ya koyar da dan Belgium din a Anderlecht. (Express)

Dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha na tunanin ci gaba da zama a Crystal Palace, kasancewar kwantiraginsa zai kare a bazaran nan. (Talksport)

Barcelona za ta sake yunkurin sayen dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Sifaniya Martin Zubimendi, mai shekara 24, a bazaran nan bayan da rahotanni suka ce Arsenal ta kasa sayensa a watan Janairu da tayin fam miliyan 53. (Express)

Dan gaban Senegal Sadio Mane, na son ci gaba da zama a Bayern Munich duk da rikicin da suka yi da Leroy Sane a watan Afirilu. (Fabrizio Romano)

Tsohon kociyan Bayern Munich Julian Nagelsmann ne zabin farko da zai maye gurbin Graham Potter, a matsayin kociyan Chelsea in ji wakilin Bajamushen. (The Times )