Karon batta tsakanin Real da Atletico a La Liga

Real Madrid vs Atletico Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid da Atletico Madrid za su fafata a wasan mako na 23 a gasar La Liga ranar Asabar a Santiago Bernabeu.

Kungiyoyin biyu su kara a wasan hamayya sau biyu a kakar nan, inda Real ta ci Atletico 2-1 a La Liga da kuma 3-1 a Copa del Rey.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona mai jan ragama.

Atletico Madrid kuwa mai maki 41 tana ta hudu a teburi, bayan kammala karawar mako na 22.

Morata da Griezmann ne kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye a La Liga, kowanne ya zura bakwai-bakwai.

Karim Benzema ne na biyu a yawan cin kwallaye a raga mai 11, biye da Robert Lewandowski na Barcelona mai 15 kawo yanzu.

Sauran 'yan Real da kowanne ya ci bakwai-bakwai a La Liga a bana sun hada da Federico Valverde da kuma Vinicius Junior.

Wasan da kungiyoyin suka fuskanci juna a bana:

2022/2023

Copa del Rey Alhamis 26 ga watan Janairu

  • Real Madrid 3 - 1 Atl Madrid

La Liga Lahadi 18 ga watan Satumbar 2022.

  • Atl Madrid 1 - 2 Real Madrid

'Yan wasan Real da za su kara da na Atletico:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. y Rüdiger.

Masu buga tsakiya Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos.

Masu cin kwallo: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Mariano, Álvaro.