Zaɓen Najeriya 2023: Muhimmancin zaɓe a addini

Bayanan bidiyo, Bayanin malamai kan zaɓen Najeriya
Zaɓen Najeriya 2023: Muhimmancin zaɓe a addini
An wallafa

A lokacin da babban zaɓen Najeriya na 2023 ke ƙara matsowa, BBC Hausa da tallafin Gidauniyar MacArthur ta haɗa wasu jerin shirye-shiryen bidiyo domin faɗakarwa da kuma fayyace wa al'umma lamurran da suka shafi zaɓen.

Abubuwan da muka taɓo sun haɗa da karɓar katin zaɓe, da rashin zuwa kaɗa ƙuri'a, da tayar da rikici da sauran su.

A wannan bidiyo, shahararrun malaman addinin musulunci biyu - Sheikh Ibrahim Maqari da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sun janyo hankalin al'umma kan muhimmancin zaɓe a addini.