Wane ne Muhammadu Buhari?

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin
Wane ne Muhammadu Buhari?
An wallafa

Tsohon shugaban Najeriya, ɗaya daga cikin ƴansiyasa na ƙasar da aka fi nuna wa ƙauna, ya rasu yana da shekara 82.

Ɗan siyasa wanda siyasarsa ta sha bamban da ta saura, ya kasance mara son hayaniya kuma mai jajircewa.

Buhari ya kasance sahun gaba a cikin shugabanni Najeriya ƙalilan da ake yi wa kallon masu gaskiya.

Tsohon babban mai taimaka masa kan yaɗa labarai Femi Adesina, ya ce "babu ta yadda za a yi ka alaƙanta Buhari da rashawa". Akasarin waɗanda ke ƙaunar Buhari sun yi hakan ne sanadiyyar ɗabi'unsa na gaskiya da son bin doka.