Mutumin da ke ƙera kayan samar da lantarki daga hasken rana a Bauchi

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Mutumin da ke ƙera kayan samar da lantarki daga hasken rana a Bauchi
An wallafa

Injiniya Abubakar Ibrahim Musa wani matashi ne a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, wanda ya ƙware wajen haɗa Sola Panel, wato faranti mai amfani da haske rana ya mayar da shi zuwa lantarki.

Ya kuma ce yana yin ƙwayayen lantarki da sauran abubuwan da suka shafi lantarki.

Matashin wanda ke karatun digirinsa na uku a fannin fasahar samar da lantarki ya ce ya haɗa gwiwwa da wani kawunsa don ƙirƙirar wani kamfanin samar da lantarki don tallafa wa al'umma da samar da ayyukan yi ga matasa.

Injiniya Abubakar ya ce wasu kayyakin aikin da suke amfani da su sukan sayo ne daga ƙasar China, yayin da wasun kuma a Najeriyar suke samunsu.

Ya ce a kowace rana suna ƙirƙirar solar panel aƙalla 60. Ya ce babban ƙalubalen da yake fuskanta a yanzu shi ne rashin ƙarfin jarin da zai bunƙasa kasuwancinsa.