Ku San Malamanku tare da Malam Usman Ibrahim Giade

Ku San Malamanku tare da Malam Usman Ibrahim Giade
An wallafa

Filin Ku San Malamanku ya karɓi baƙuncin Malam Usman Ibrahim Sulaiman Giade, wanda aka fi sani da Usman Ibrahim Giade.

Shehin malamin haifaffen garin Giade ne da ke ƙaramar hukumar Giade ta jihar Bauchi a arewacin Najeriya. An haife shi a shekarar 1976.

Ya je gururuwa da dama neman ilimi kamar garin Zariya inda ya yi karatun Fiƙihu a wajen Sheikh Tijjani Abdulkadir Zariya.