Haɗarin mota ba zai hana ni taka leda ba - Antonio

Asalin hoton, Getty Images
Michail Antonio ya ce haɗarin mota da ya yi da ta kai ya karya kafa a cikin watan Disamba ba zai hana shi taka leda ba, wanda ke jinya.
Mai shekara 34 an kai shi asibiti ranar 7 ga watan Disamba a haɗarin mota da ya je ya bugi bishiya, wanda sai da ƙyar ƴan kwana-kwana suka zaƙulo shi.
Ya fara fita motsa jiki, har an yi masa tarbar girma a filin wasa na London Stadium ranar Litinin, inda magoya baya suka yi ta masa tafi.
A ranar ta Litinin West Ham ta yi rashin nasara 1-0 a hannuun Newcastle United a gasar Premier.
A wata hira da aka yi da Antonia a BBC ya ce ''Ina da tabbaci 100 cikin 100 zan koma taka leda kamar yadda na saba. Abin da na sa a gabana kenan.''
A makon nan kociyan West Ham, Graham Potter bai fayyace lokacin da Antonia zai koma taka leda ba.
Ya kara da cewar baya son ya sa wa Antonio matsi, gwara ya samu lokacin mai tsawo da zai murmure yadda ya kamata.
Antonio shi ne kan gaba a ci wa West Ham ƙwallaye a tarihi mai 68 a raga.










