Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Akanji zai yi jinyar makonni 10
Dan ƙwallon Manchester City, Manuel Akanji zai buƙaci tiyata a cinyarsa, lamarin da zai sa ya yi jinyar aƙalla makonni 10.
Dan ƙasar Switzerland ɗin mai shekaru 29 ya ji raunin ne a ranar Talata a gasar Champions league da Real Madrid ta doke City da ci uku da biyu.
"Za a yi masa tiyata a ranar Asabar, kuma jinyar za ta kai ta mako takwas zuwa goma," in ji manajansa Pep Guardiola.
An soma wasa 20 cikin 24 tare da Akanji a gasar Premier ta bana kuma ya buga wasa 30 a gasa daban-daban.
Akanji ya shiga rukuni ɗaya da irin su John Stones, Nathan Ake da kuma Ruben Dias da ke jinya a City.
Shi ma Jack Grealish ya ji rauni a lokacin wasan amma bai yi muni ba.
Kocinsa Guardiola ya ce ɗan ƙwallon Ingilan ba zai buga wasansu da New Castle ba a ranar Asabar.