Bikin wasa da tumatur mafi girma na duniya a Spain

Bayanan bidiyo, Bikin wasa da tumatur na duniya a Spain
Bikin wasa da tumatur mafi girma na duniya a Spain
An wallafa

Bikin wasa da tumatur mafi girma da ake yi a garin Buñol kusa da Valencia a ƙasar Spain ya dawo a bana, bayan shafe sgekara biyu ba a yi ba saboda annobar cutar korona.

Wani bidiyo ya nuna yadda dubban mutane suke wasa da tumatur tare da yin faca-faca da shi a jikinsu a lokacin bikin da aka ayyana shi a matsayin bikin wasan abinci mafi girma.

Mazauna garin ne suka fara ƙirƙirar yin bikin a tsakaninsu a shakrar 1945.