Indiya: Ana kwashe gwamman mutane daga garin da ke nutsewa

Asalin hoton, Getty Images
An fara kwashe gwamman iyalai daga garin Joshimath na jihar Uttarakhand da ke ƙasar Indiya bayan da gidaje tare da titunan garin suka ci gaba da tsagewa.
Tuni dai aka ayyana garin da cewa na cikin ''mummunan bala'i'' kamar yadda wani jami'in gundumar ya bayyana.
Fiye da gidaje 600 ne suka tsage kawo yanzu saboda naso wanda kuma sannu-a-hankali ke haifar da nutsewar gidajen.
Jami'ai sun ce suna ƙoƙarin samar da na'urorin da za su riƙa busar da nason gidajen, tare da taimakon kuɗi ga iyalan da lamarin ya shafa.
Tawagogin gwamnatin tarayya biyu na kan hanyarsu ta zuwa garin domin duba yanayin da garin ke ciki, kamar yadda wani jami'i ya bayyana.
Kusan iyalai 68 ne aka kwashe daga garin zuwa wani wuri na wucin-gadi da aka shirya a otal-otal da kuma gidajen saukar baƙi.
Kuma jami'an sun ce za a kwashe mutane da dama a cikin 'yan kwanakin nan.
Mazauna garin sun kwashe watanni suna kira game da wannan barazana da suke fuskanta, to amma lamarin ya yaɗu a 'yan kwanankin nan ne bayan da gidajen suka fara tsagewa, sannan kuma kafafen yaɗa labarai suka fara yaɗa labaran abubuwan da ke faruwa kan lamarin.
A makon da ya gabata, jami'ai suka dakatar da gine-gine a garin bayan da dubban masu zanga-zanga suka toshe babbar hanyar ƙasar.
Masu zanga-zanga sun ɗora alhakin matsalar kan yawan gine-gine.
Tawagar ƙwararru ta ziyarci garin cikin makon da ya gabata sannan kuma ta gabatar da rahotonta ga gwamnati.
To sai dai ba a saki rahoton ga sauran al'umma ba ya zuwa yanzu, to sai dai Jaridar Time ta ƙasar Indiya wadda ta samu kwafin rahoton, ta ruwaito cewa tawagar ƙwararrun ta buƙaci da a rushe duka gidajen da suka nuna 'babbar alamar tsagewa'.
Haka kuma Jaridar ta ambato wani babban jami'i na cewa akalla kashi 25 cikin 100 na gidajen garin na fuskantar matsalar naso.
To amma BBC ba ta tabbatar da wannan iƙirari ba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matsalar naso a garin ta faro tun gwamman shekaru da suka gabata, a shekarar 1976 gwamnati ta kafa kwamiti domin duba matsalar nutsewar gidaje a garin Joshimath bayan da mazauna garin sun kai ƙorafin tsagewar gidajensu.
A rahoton da kwamitin ya gabatar a wancan lokacin ya yi gargaɗin yin manyan gine-gine a yankin.
To amma cikin shekaru da dama tun wancan lokacin, an dakatar da gine-ginen ne kawai a Uttarakhland, wanda ke yankin Himalaya.
Jihar na da tarihin tsofaffin malaman addinin Hindu, don haka jihar na samun miliyoyin masu ziyarar bauta a duk shekara.
Masana na cewa yawan gine-gine na lalata yanayin ƙasar yankin, lamarin da zai iya haifar da naso da kuma girgizar ƙasa.
A ranar Lahadi ofishin Firaministan ƙasar ya ce wasu hukumomin tarayya na aiki da gwamnatin jihar Uttarakhand domin magance matsalar tare da tabbatar da kariya ga mazauna yankin.
Shugaban addinin Hindu ya kuma nemi babbar kotun ƙolin ƙasar ta gaggauta sa-baki tare da ayyana matsalar da cewa "mummunan bala'i'' ne ga ƙasa.

A cikin watan Oktoba BBC ta ziyarci garin tare da zantawa da mazauna yankin waɗanda ke zaune cikin fargaba.
''Mun fice daga gidanmu a lokacin da aka fara ruwan sama saboda muna fargaba'', in ji Sumedha Bhatt, wanda ke zaune a ƙauyen Ravigram.
Sannan kuma a lokacin wannan ziyara BBC ta haɗu da mutane da dama waɗanda suka fara guje wa gidajensu saboda yadda tsagewar gidajen nasu ta fara yawaita sakamon saukar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Inda wasu kuma suka riƙa nema wa kansu mafita ta hanyar amfani da fallen kwano da katako domin tallafa wa gidajen nasu.











