Watakila Arsenal ta lashe Champions League a bana - Henry

Asalin hoton, Getty Images
Da ƙyar idan Arsenal za ta ɗauki Premier League na bana, amma tana turbar lashe Champions League in ji Thierry Henry.
Ranar Talata Gunners ta je ta ɗura 7-1 a ragar PSV Eindhoven a wasan farko zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.
Kawo yanzu kafar Arsenal ɗaya ta kai zagayen kwata fainal a Champions League, wadda za ta fuskanci wadda ta yi nasara tsakanin Real ko Atletico a watan Afirilu.
A ranar ta Talata Real ta yi nasara 2-1 a kan Atletico a wasan hamayya na ƴan birnin Madrid da suka kece raini a Santiago Bernabeu a gasar ta zakarun Turai.
Rawar da Arsenal ta taka ranar Talata a Netherlands ya sa ana ganin ƙungiyar Emirates za ta iya abin kirki a sauran wasannin da suke gabanta a gasar.
Henry, shi ne kan gaba a yawan ci wa Arsenal ƙwallaye a tarihi, wanda ya buga wasan karshe a Champions League a 2006 da Barcelona ta yi nasara.
''Bayan da aka fitar da Arsenal daga FA da Carabao Cup a a bana da ƙyar idan za ta lashe Premier, kenan za ta mayar da karfinta a gasar zakarun Turai,'' in ji Henry.
''Haka zai sa su iya lashe Champions League, kamar yadda Henry ya sanar a hira da CBS Sports Golazo. "Na yadda da hakan, shi ya sa nake da ƙwarin gwiwa.
''Ba zan kaskantar da Eindhoven ba, tun farko na ɗauka karawar mai sarkakiya ce, musamman a gidansu, amma sai wasan ya yi sauki, sun taka rawar gani.''
Tsohon ɗan wasan Barcelona ya kara da cewar rawar da Arsenal ta taka a Eindhoven ya kara mata kwarin gwiwa sosai.
Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier League da tazarar maki 13 tsakani da Liverpool mai jan ragama.
Ranar Lahadi Arsenal za ta je gidan Manchester United, domin buga wasan mako na 28 a Champions League.
Daga nan Gunners za ta karɓi bakuncin wasa na biyu da PSV Eindhoven zagayen ƴan 16 a Champions League ranar Laraba 11 ga watan Maris.











