Abubuwan da ya kamata ku sani kan wasan ƙarshe na Club World Cup

Club world cup

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A yau, Lahadi 17 ga watan Yuli ne za a fafata wasan ƙarshe na gasar cin kofin FIFA Club World Cup, inda za a kece raini tsakanin ƙungiyar Paris Saint-Germain wato PSG ta Faransa da ƙungiyar Chelsea ta Ingila.

Za a buga wasan na ƙarshe ne a filin wasa MetLife Stadium domin kawo ƙarshen sabon tsarin gasar, wanda ƙungiyoyi 32 suka fafata, maimakon ƙungiyoyi zakarun nahiyoyi da ake yi a baya.

Fifa ce ta zaƙulo ƙungiyoyin tamaula 32 da aka zaɓo daga nahiya shida da suka haɗa da Asia da Afirka da Arewa da tsakiyar Amurka da yankin Caribbean da Kudancin Amurka da Oceania da kuma Turai.

An buga wasannin ne a Amurka daga ranar 14 ga watan Yuni zuwa yau, 13 ga watan Yulin 2025 a filaye 12 a faɗin ƙasar.

An fara gudanar da gasar a 2000 a Brazil kuma Corinthians ce ta fara lashe kofin, bayan nasara a kan Vasco da Gama 4-3 a bugun fenariti a wasan ƙarshe.

Gasar ta wannan karon, bayan tsawaita shi da aka yi, ƴanwasa da ƙungiyoyi sun yi ƙorafin yanayin zafin Amurka, da kuma rashin halartar masu kallo da yawa.

PSG ta lashe gasar Ligue 1 da Coupe de France da Champions League a bana, ita kuma Chelsea na fafatukar kafa wani sabon tarihi ne na zama ƙungiyar da ta lashe dukkan kofunan nahiyar turai bayan ta lashe gasar UEFA Conference League a watan Mayu, kasancewar ta taɓa zakarun turai da gasar europa.

Kwatanta ƙungiyoyin biyu

Idan PG ta lashe wannan kofin, zai zama ta lashe kofuna guda biyar ke nan a kakar bana.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙungiyar ta lashe kofin Trophee des Champions a watan Janairu, da gasar Ligue 1 a watan Afrilu tun ana saura wasa shida a ƙarƙare gasar, da kofin Coupe de France da gasar UEFA Champions League a watan Mayu.

Babu ƙungiyar da ta kai PSG lashe kofuna a cikin ƙungiyoyi 31 da suka buga gasar. Ita kuma Chelsea ta lashe kofin UEFA Conference League ne a kakar.

Chelsea ta zura ƙwallo uku daga wajen layin 18 a wannan gasar : Tyrique George a wasan ƙungiyar da Espérance da Reece James a ragar Benfica sai Joao Pedro a wasansu da Fluminense FC.

Ita kuma PSG ƙwallo biyu ne ta jefa daga wajen 18: Fabian Ruiz a a wasan ƙungiyar da Atlético de Madrid da Desire Doue a wasansu da Bayern München.

Chelsea ta lashe gasar zakarun turai guda biyu, ita kuma PSG ta lashe sau ɗaya ne.

Chelsea ta lashe kofin a kakar 2011/12 duk ta ƙare a ta huɗu a gasar premier league a shekarar.

Sannan ta lashe gasar a karo na biyu a kakar 2020/21 bayan ta ƙare a ta huɗu a gasar premier.

Ita kuma PSG ta lashe kofin na zakarun turai ne a bana bayan doke Inter Milan a wasan ƙarshe.

Yadda ƙungiyoyin suka kai wasan ƙarshe

Tun farkon gasar ne dai PSG take nuna bajinta, sannan ta doke manyan ƙungiyoyi irin su Atlético Madrid da Bayern Munich da Real Madrid.

Sai dai a wasannin rukuni ƙungiyar Botafogo ta mata ci ɗaya mai ban haushi, wanda ke nuna duk da ganiyarta, ba ta fi ƙarfin kaye ba.

Ita kuma Chelsea da ƙyar ta tsallake zuwa wasannin ƴan 16, inda sai ta doke Esperance Sportive de Tunis bayan ƙungiyar Flamengo ta doke ta 3-1. Sai dai tun da ta fara wasannin zagaye na biyu ne take nuna ƙwarewa har ta kai wasan ƙarshe.

Fitattun ƴanwasan ƙungiyoyin

Da zarar an yi maganar PSG, Ousmane Dembele ne yake fara zuwa tunanin mutane, wanda har ake masa tunanin lashe kyautar Ballon d'Or ta bana.

Ɗanwasan mai shekara 28 ya zura ƙwallo 35, sannan ya taimaka an zura ƙwallo 14 a wasa 52 da ya buga wa ƙungiyar a kakar bana.

Dembele bai cimma ganiyarsa ba a Barcelona bayan ta zuba maƙudan kuɗi wajen ɗauko shi daga Dormund a shekarar 2018, amma tun komawarsa PSG a 2023, sai aka fara ganin alamar ƙwarewa.

Idan kuma aka jiaye Dembele, PSG tana da zaratan ƴanwasan irin su Kvaratskhelia da Doué da Ruiz da Vitinha da Neves da du suke ganiya. Sannan suna da ƴanwasan baya biyu: Achraf Hakimi da Nuno Mendes waɗanda suke ci, su hana a ci gidansu.

A baya, Cole Palmer ne ke jan ragamar Chelsea, amma ƙungiyar ta ɗauko Jao Pedro a kan fam miliyan 55, wanda kuma ya fara da ƙafar dama, wanda hakan ya sa gabanta ya ƙara ƙarfi sosai.

Sai dai ƙungiyar na cikin damuwar yiwuwar rashin ɗanwasa Moisés Caicedo, wanda ya samu rauni a wasan kus da ƙarshe.