Barcelona ta yi wasa 22 a jere ba tare da an doke ta ba

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga, bayan tashi 1-1 da Real Betis a gida ranar Asabar a karawar mako na 30 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Wasa na 22 da ta yi a jere a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba kenan kawo yanzu, wadda ta yi canjaras na huɗu daga ciki.
Rabon da Barcelona ta yi rashin nasara tun 2-1 da Atletico Madrid ta doke ta a gida a La Liga ranar 21 ga watan Disambar 2024.
Barcelona wadda ba a doke ba tun da aka shiga 2025, ta yi 1-1 da Getafe a La Liga ranar 18 ga Janairu da 2-2 da Atalanta a Champions League ranar 29 ga Janairu.
Haka kuma ƙungiyar da Hansi Flick ke jan ragama ta yi 4-4 da Atletico Madrid a Copa del Rey wasan farko zagayen daf da karshe cikin Fabrairu da wanda ta tashi 1-1 da Betis a La Liga daga wasa 22 a jere ba tare da rashin nasara ba.
Barcelona wadda ta lashe Spanish Super Cup a bana, ta yi nasara 21 a La Liga daga karawa 30 da canjaras huɗu aka doke ta fafatawa biyar.
Haka kuma Barcelona ce kan gaba a yawan cin ƙwallaye a La Liga mai 83 a raga aka zura mata 24, Robert Lewandowski ne kan gaba a cin ƙwallaye daga Barca mai 25 a raga.
Wasan da suka rage wa Barcelona a bana
La Liga ranar Asabar 5 ga watan Afirilu
- Barcelona da Real Betis
Champions League ranar Laraba 9 ga watan Afirilu
- Barcelona da Borussia Dortmund
La Liga ranar Asabar 12 ga watan Afirilu
- Leganes da Barcelona
Champions League ranar Talata 15 ga watan Afirilu
- Borussia Dortmund da Barcelona
La Liga ranar Asabar 19 ga watan Afirilu
- Barcelona da Celta Vigo
La Liga ranar Talata 22 ga watan Afirilu
- Barcelona da Mallorca
Wasan karshe Copa del Rey Asabar 26 ga watan Afirilu
- Barcelona da Real Madrid
La Liga ranar Lahadi 4 ga watan Mayu
- Valladolid da Barcelona
La Liga ranar Lahadi 11 ga watan Mayu
- Barcelona da Real Madrid
La Liga ranar Laraba 14 ga watan Mayu
- Espanyol da Barcelona
La Liga ranar Lahadi 18 ga watan Mayu
- Barcelona da Villarreal
La Liga ranar Lahadi 25 ga watan Mayu
- Ath Bilbao da Barcelona










