Ranar Mata ta Duniya 2023: Hanyoyin da mata za su taimaka wa junansu
Ranar Mata ta Duniya 2023: Hanyoyin da mata za su taimaka wa junansu
An wallafa
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 8 ga watan Maris ɗin kowacce shekara a matsayin ranar mata ta duniya.
Taken ranar ta 2023 shi ne DigitALL: Ƙirƙira da fasaha domin samar da daidaito tsakanin jinsi.
Ana bikin ranar domin tattauna batutuwan da suka shafi haƙƙoƙin mata da kuma irin cin zarafin da suke fuskanta.
A wannan bidiyon, BBC ta tattauna da Sabiha Hussain, wata likita da ta shahara a shafukan sada zumunta inda ta yi ƙarin haske game da muhimmancin ranar da kuma hanyoyin inganta rayuwar mata ta yadda za su iya dogaro da kansu.



