'Ƙabilu kusan 40 ne a ƙarƙashin sarkin Hausawan Zango a Ghana'

'Ƙabilu kusan 40 ne a ƙarƙashin sarkin Hausawan Zango a Ghana'
An wallafa

Sarkin Hausawan Zangon Ashanti da ke birnin Kumasi na Ghana, Alhaji Umar Farouk Saeed, ya shaida wa BBC Hausa cewa akwai ƙabilu kusan 40 da ke ƙarƙashin mulkinsa.

Sarkin ya ce Hausawan Ghana sun yi auratayya tsakaninsu da sauran ƙabilu, ciki har da shi kansa inda mahaifiyarsa ‘yar ƙabilar Gwanjawa ce da ke Ghana.

“Ko’ina ka yi Hausa za ka samu mai jin Hausa, daga cikin ƙabilun ma da suke garin nan akwai waɗanda ba sa jin wani harshe sai Hausa,” in ji mai matarban.

Ya ƙara da cewa: “Ƙasarmu ta biyu ita ce Najeriya, ta farko Ghana.”