'Da sana'ar nan nake taimaka wa 'ya'yana duk da nakasar da nake da ita'

'Da sana'ar nan nake taimaka wa 'ya'yana duk da nakasar da nake da ita'
An wallafa

Albarkacin Ranar Cutar Shan-Inna (foliyo) ta Duniya da aka ware duk ranar 24 ga watan Oktoba, Sa'adatu Bashir mai larurar nakasa a Abuja babban birnin Najeriya, ta faɗa wa BBC Hausa cewa ba da lalurar aka haife ta ba.

Sa'adatu ta ce ta gamu da larurar tana 'yar shekara bakwai da haihuwa, abin da ya sa ke nan ta dage da yi wa dukkan 'ya'yanta bakwai rigakafin cutar.

Matar wadda 'yar asalin Jihar Binuwai ce a tsakiyar Najeriya, ta ce ta zaɓi ta yi sana'a saɓanin yin bara don ta taimaka wa 'ya'yanta su samu rayuwa mai kyau.

Kaɗan ya rage a kawar da cutar ta foliyo - wadda ƙwayar cuta ke haifarwa - daga duniya baki ɗaya. A yanzu ta fi ƙamari a ƙasashen Pakistan da Afghanistan.

Akan kamu da cutar ta hanyar taɓa wani abu da ya fito daga jikin mai ɗauke da- kamar gurɓataccen abinci ko ruwan sha - ko kuma bayan sun yi atishawa ko tari.