Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙin Tigray: Yadda yunwa ke kashe yara, wasu dubbai suka zama mabarata
Yaƙin Tigray: Yadda yunwa ke kashe yara, wasu dubbai suka zama mabarata
An wallafa
Rahoto na musamman da sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya yi ya gano yadda yunwa ke kashe yara, wasu dubbai kuma suka zama mabarata saboda yaƙi a yankin Tigray na Ethiopia (Habasha).
Tun a watan Yunin 2021 gwamnatin tarayyar Habasha ta toshe yankin Tigray, inda tungar 'yan tawayen TPLF take, kuma yanayin rayuwa yana ta ta'azzara tun daga lokacin.
Matakin ya sa ba a iya shigar da kayayyakin yau da kullum, ciki har da abinci da kayayyakin aikin lafiya.
A wannan rahoton, za a ga yadda ƙananan yara ke mutuwa saboda yunwa sannan wasu dubbai suka koma bara a tituna.