Real na ci gaba da shirin karɓar bakuncin Arsenal ranar Laraba

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na ci gaba da shirye-shiryen karɓar bakuncin Arsenal a Champions League ranar Laraba a Santiago Bernabeu.
Arsenal, wadda ta doke Real Madrid 3-0 a makon jiya za ta je Sifaniya, domin buga wasa na biyu zagayen kwata fainal a gasar ta zakarun Turai ta kakar nan.
Real ta yi atisaye ranar Litinin, inda ƴan wasa suka motsa jiki da guje-guje, domin samun kuzarin da suke bukata a wasan da Gunners.
Sai dai wasu daga cikin ƴan wasan sun yi atisaye a rufaffen ɗaki, kenan waɗanda ke jinya da ba su kammala murmurewa ba.
Daga cikin masu jinya a Real Madrid sun haɗa da Mendy da kuma mai tsare raga, Andriy Lunin.
Sauran ƴan wasan Real Madrid sun buga ƙwallo a tsakaninsu, inda aka raba filin gida biyu, bayan nan aka koma gwada gola, sannan wasu suka yi wasa da tamaula.
Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin La Liga na fatan kai wa zagayen daf da karshe a Champions League a bana, wadda take rike da kofin bara.
Haka kuma Real za ta yi wasa da Gunners ba tare da Camavinga ba, wanda aka bai wa jan kati a Emirates.
Kylian Mbappe zai yi wa Real Madrid fafatawar, wanda ya yi ketar da aka yi masa jan kati ranar Lahadi a wasan La Liga da Deportivo Alaves.
Real wadda ta ci Alaves 1-0 a wasan mako na 31 a La Liga tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama.










