Man City ta ci ribar kasuwancin kakar 2021/22

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta sanar da samun kudin shiga da ya kai £613m da kuma cin ribar £41.73m a kakar 2021-22.
Shi ne kudin shiga mai tsoka na biyu da aka samu a tarihin kungiyoyin tamaular Ingila, bayan Manchester United a kakar 2019 da ta samu £627m.
City ta lashe Premier League na shida a tarihi, tun bayan da aka cefanar da kungiyar ga rukunan attajiran Abu Dhabi United.
Kudin shigar City ya kai £43.2m tun daga bayan da aka buga wasanni ba 'yan kallo, sakamakon gudun yada cutar korona.
Bayan da aka koma kallon tamaula a sitadiya City ta samu kudin shiga £54.5m kudin shiga kallon wasanninta kenan.
Ta kuma samu karin riba daga kudin tallace - tallace £271.7m zuwa £309.5m daga shekarar da ta gabata.
City tana ta biyu a kan teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal a bana, bayan wasa 12 a babbar gasar tamaula ta Ingila.







