Burina shi ne matasa su samu abin dogaro da kai - Sarkin Dutse
Burina shi ne matasa su samu abin dogaro da kai - Sarkin Dutse
An wallafa
A ranar biyar ga watan Fabarairu ne aka naɗa Alhaji Hamim Nuhu Muhammadu Sanusi a matsayin sabon sarkin Dutse bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi.
A tattaunawarsa da BBC watannin uku bayan hawansa kan karagar mulkin masarautar, sabon sarkin ya ce zai ƙara himma wajen haɗa kan al'umma da zaburar da matasa wajen neman na kansu.
Sabon sarkin ya ce a lokacin da aka naɗa shi sarki ya ji daɗi, domin kuwa a cewarsa burin kowanne ɗan sarki, shi ne ya zama sarki.
Ya ce yana godiya da fatan alheri da waɗanda suke ba shi goyon baya, wajen gudanar da al'amura.



