Ten Hag ya kwatanta salon kwallon Rashford iri daya da ta Mbappe

An wallafa

Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya ce irin salon kwallon da Kylian Mbappe ke buga wa daya ce da ta Marcus Rashford na Ingila.

Rashford shi ne kan gaba a ci wa Ingila kwallaye a raga a Gasar Kofin Duniya a Qatar, bayan da Faransa ta yi waje da ita daga wasannin ranar Asabar.

''Idan Marcus ya dunfari 'yan baya da tamaula, ba mai irin salon da yake yi a duniya, sai dan wasa daya tilo a duniya wato Kylian Mbappe.''

Rashford zai koma buga wa Manchester United Premier League da za a ci gaba ranar 26 ga watan Disamba, bayan kammala hutun Gasar Kofin Duniya.

Dan kwallon United bai taka rawar gani ba a kakar bara - dan wasan ya fuskanci kalubale bayan da ba a fara kakar tamaula da shi ba, sakamakon jinyar allon kafada.

Rashford ya ci kwallo hudu a karawa 25 a Premier League - karon farko da bai zura sama da 10 a raga ba tun 2017/18, sannan ya rasa gurbinsa a tawagar Ingila.

Sai dai dan wasan ya koma kan ganiya karkashin sabon kociya Ten Hag a kakarsa ta farko a United a bana, inda Rashford ya zura takwas a wasa 19.

Kwallo hudun da dan wasan mai shekara 25 ya ci kawo yanzu a Lik ya zura iri daya da ya yi a kakar 2021-22.

Kociyan United ya bayar da misalin kwallon da Phil Foden ya ci Wales a Qatar da kwarewar Rashford da ya sa a wasannin Ingila.