An ci ƙwallo takwas a wasan Barca da Atletico a Copa del Rey

Rodri

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona da Atletico Madrid sun tashi 4-4 a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey ranar Talata a Estadi Olimpic Lluis Companys.

Minti ɗaya da take leda Atletico ta fara cin ƙwallo ta hannun Alvarez, sannan Griezmann ya kara na biyu a minti na biyar tsakani.

Barcelona ta zare ɗaya ta hannun Pedri a minti na 19, sannan Cubarsi ya farke na biyu minti uku tsakani.

Kafin hutu Barcelona ta kara na uku ta hannun Martinez, haka suka je zagayen farko Barcelona na cin 3-2.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, sai Barcelona ta ci na hudu a karawar ta hannun Lewandowski kai kace an tashi da Atletico Madrid a wasan.

Daga baya kungiyar da Diego Simeone ke jan ragama ta zare na uku ta hannun Llorente daga baya ta zare na huɗu ta hannun Sørloth.

Wannan shi ne karo na biyu da suka kece raini a tsakaninsu a bana, bayan daAtletico ta je ta doke Barcelona a La Liga ranar 21 ga watan Disamba.

Ranar Laraba 4 ga watan Afirilu, Atletico za ta karɓi bakuncin wasa na biyu a daf da karshe a Copa del Rey.

Ranar Laraba 27 ga watan Fabrairu za a kara a ɗaya wasan daf da karshe a kofin tsakanin Real Sociedad da Real Madrid.

Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 54, iri ɗaya da na Real Madrid ta biyu da kuma Atletico mai maki 53 ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.