Real Madrid na kwadayin Haaland, PSG na farautar Maguire

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na duba yiwuwar dauko ɗan wasan Manchester City kuma ɗan asalin Norway Erling Haaland mai shekara 22, a wani ɓangare na shirin dauko matasa da ke tashe kungiyarta, kamar yada take harin ɗan wasan Borussia Dortmund Jude Bellingham ɗan kasar Ingila mai shekara 19.(Independent)
Ɗwasan Manchester United kuma mai tsaron baya a Ingila Harry Maguire, mai shekara 30, ya kasance wanda Paris St-Germain ke kwaɗayi a kan fam miliyan 50.(Sun)
Mutumin da aka bai wa shugabanci Bayern Munich Uli Hoeness, ya ce zai kasance "abin bajinta idan kungiyar ta Jamus ta dauko ɗan wasan Tottenham, asalin kasar Ingila Harry Kane, mai shekara 29, kuma lokacin da kungiyar za ta kashe yuro miliyan 100 kan ɗan wasa ya tunkaro". (Sky Sport Germany - in German)
Manchester United ta sanya sunan ɗan wasan Chelsea da Ingila Mason Mount, mai shekara 24, cikin jeren 'yan wasan da take hari a wannan kaka. (Guardian)
Mauricio Pochettino ya shaidawa Tottenham cewa ya matsu ya koma domin maye gurbin Antonio Conte a masatyin koci, sai dai mutumin mai shekara 51 asalin kasar Argentine na da zaɓin samun wata kungiya a wajen Ingila. (talkSPORT)
Tottenham za ta tattauna kan cancantar Pochettino da Thomas Tuchel a matsayin wanda ya fi dacewa ya maye gurbin Conte, wanda kungiyar ke Shirin raba gari da shi. (Guardian)
Kocin Brentford Thomas Frank da na Fulham Marco Silva na cikin jeren mutane biyar da ake nazarin tantacewa domin maye gurbin Conte aTottenham. (Independent)
Manchester City ta shirya tsaf domin sayar da ɗan wasanta na baya kuma ɗan kasar Sifaniya Aymeric Laporte, mai shekara 28, a wannan kaka muddin ta iya farauto masu maye gurbinsa. (Football Insider)
Manchester United na ɗaya daga cikin kungiyoyi da ke nuna zawarci kan ɗan wasan Argentina mai shekara 29 Paulo Dybala, da take iya sayowa kan fam miliyan 11 a wannan kaka duk da cewa a bara ya koma Roma. (Goal)
Manchester United ta shiga jeren masu nuna kwaɗayinsu kan mai tsaron raga a Brentford David Raya, ɗan wasan mai shekara 27 na Shirin raba gari da kungiyarsa bayan watsi da sabon kwantiraginsa. (talkSPORT)

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dan wasan baya a Manchester City Joao Cancelo, mai shekara 28, ya kasance wanda Barcelona ke Shirin daukowa, idan ya ƙare zamansa na aro a Bayern Munich a wannan kaka. (Sport - in Spanish)
Wolves a shirye take ta sake gabatar da sabon tayi na fam miliyan 20 kan ɗan wasan Bristol City, yayinda da suke kokarin ganin sun sha gaban Tottenham da West Ham a farautar ɗan wasan mai shekara 19 daga Ingila. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan gaba a Argentina Lionel Messi, mai shekara 35, na tattaunawa kan sabon kwantiragi da Paris St-Germain, amma ɗan wasan Faransa mai shekara 24 Kylian Mbappe, da na Brazil mai shekara 31, Neymar, na iya raba gari da kungiyar ta Lig 1 a wannan kaka. (Mail)
Newcastle United ta shirya tsaf domin shiga a fafata da ita a zawarcin ɗan wasan Southampton, James Ward-Prowse, mai shekara 28. (Football Insider)
Newcastle na kan gaɓar amincewa da sabon kwantiragi mai tsayi da ɗan wasan Brazil mai buga tsakiya Bruno Guimaraes. (Telegraph - subscription required)
Inter Milan ta gabatar da tayin sabon kwantiragi shekara ɗaya kan Edin Dzeko amma ɗan wasan na Bosnia mai shekara 36, ya fi son kwantiragi ya kai na shekara biyu don haka yana iya tafiya West Ham. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Bayer Leverkusen na iya shiga farautar ɗan wasan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 22, idan kwantiraginsa ya ƙare da Chelsea a wannan kaka. (Sky Sport Germany - in German)
Dan wasan tsakiya a Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 25, ya nesanta kansa da batun komawa Manchester United. (RAC1, via Goal)
Leeds na kan gaba a gabatar da tayi kan ɗan wasan Barcelona Ilias Akhomach, mai shekara 18. (Sport - in Spanish)
Arsenal da Chelsea sun shiga rukunnin kungiyoyin da ke nuna kwaɗayinsu kan ɗan wasan Brazil Vitor Roque daga Athletico Paranaense. (90min)
Paris St-Germain na duba yiwuwar dauko sabon koci domin maye gurbin Christophe Galtier, hankalinsu na kan Thomas Tuchel, wanda har yanzu ba shi da aiki bayan korarsa da Chelsea tayi a Satumban bara. (Relevo - in Spanish)









