Arsenal ta caskara Barcelona 5-3 a Amurka

An wallafa

Arsenal ta casa Barcelona da ci 5-3 a wasan atisayen tunkarar kakar da za a fara watan gobe da suka fafata a SoFi Stadium a birnin Los Angeles.

Minti bakwai da fara wasan Barcelona ta ci kwallo ta hannun Robert Lewandowski daga baya Arsenal ta farke ta hannun Bukayo Saka a minti na 13.

Barcelona ta kara kwallo ta hannun Raphinha, amma kafin hutu Gunners ta farke ta hannun Kai Havertz, dan wasan da ta dauka a bana daga Chelsea.

Arsenal ta kara kwallo biyu a ragar kungiyar ta Camp Nou ta hannun Leandro Trossard, wanda shi ne ya ci kwallaye biyu.

Daga baya ne Barcelona ta zare daya ta hannun Ferran Torres, sai dai Gunners ta kara na biyar ta hannun Fabio Vieira.

Arsenal, wadda ta yi ta biyu a gasar Premier League da ta wuce za ta fara kakar bana ranar 6 ga watan Agusta.

Gunners din za ta kece raini da Manchester City a Community Shield.

City ce ta lashe Premier League da FA Cup da Champions League a 2022/23.