Zwayer ne zai busa wasan Real da Liverpool ranar Laraba

Felix Zwayer

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Felix Zwayer ne zai yi alkalancin wasan da Real Madrid za ta karbi bakuncin Liverpool a Champions League ranar Laraba.

Wannan shine wasa na biyu da za su kara a bana a zagaye na biyu gurbin 'yan 16 a gasar zakarun Turai da za su kece raini a Santiago Bernabeu.

Raflin dan kasar Jamus zai yi alkalancin wasan Real Madrid karo na biyu a gasar ta zakarun Turai.

Shine ya busa wasan cikin rukuni a Champions League da Real Madrid ta casa Galatasaray 6-0 a kakar 2019/20.

Kungiyar Sifaniya da ta Ingila sun kara ranar 21 ga watan Fabrairu a Anfield a wasan farko, inda Real ta yi nasara da cin 5-2.

Liverpool ce ta fara zura kwallo biyu a raga ta hannun Darwin Nunez da Mohamed Salah.

Daga baya Real ta ci biyar ta hannun Vinicius Junior da ya zura biyu a raga da Eder Militao mai daya da kuma Karim Benzema da shima ya ci biyu.

Ko a bara a wasan karshe da suka buga a Faransa, Real ce ta ci Liverpool 1-0 ta dauki Champions League na 14 jimilla.

Liverpool tana da kofin zakarun Turai shida a tarihi, amma na karshe da ta dauka shine a 2018/19 da ta ci Tottenham 2-0.