Man City za ta yi wasa shida a jere masu zafi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City za ta buga wasa shida a jere masu zafi da ya hada da biyu a Champions League da guda huɗu a Premier League.

Ƙungiyar Etihad za ta kece raini gida da waje da Real Madrid a Champions League, sannan ta kara da Newcastle da Liverpool ta Tottenham da kuma Nottingham Forest a Premier.

City za ta fara karɓar bakuncin Real Madrid a wasan farko a Champions League karawar cike gurbi ranar Talata 11 ga watan Fabrairu

City ta kasa kai wa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai ta bana, bayan da ta kare a mataki na 22 a teburi, Real kuwa mai rike da kofin ta yi ta 11.

Ƙungiyoyin biyu sun kara sau 12 a tsakaninsu, inda City ta yi nasara hudu da canjaras biyar, Real ta ci wasa uku.

Wasan karshe da suka haɗu a tsakaninsu a Champions League:

2023/2024

Champions League Ranar Laraba 17 ga watan Afirilu 2024

  • Man City 1 - 1 Real Madrid

Champions League Ranar Talata 9 ga watan Afirilun 2024

  • Real Madrid 3 - 3 Man City

Wasa na biyu shi ne a Premier League da City za ta yi ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu, inda za ta karɓi bakuncin Newcastle.

Newcaste da City sun tashi 1-1 a wasan farko a St James's Park a Premier League a bana ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.

Newcastle ce ta shida a teburin Premier da maki 41 iri ɗaya da na City, wadda take ta biyar ɗin teburi.

Daga nan ne City za ta je Sifaniya, domin buga wasa na biyu na cike gurbi a Champions League da Real Madrid mai rike da kofin ranar 19 ga watan Fabrairu.

Wasa na huɗu kuwa da City za ta yi shi ne karɓara bakuncin Liverpool a Premier League ranar 23 ga watan Fabrairu.

Liverpool ce ta ɗaya a kan teburi da maki 56, ita kuwa City tana ta biyar da maki 41.

Ranar 1 ga watan Disambar 2024, Liverpool ta doke City 2-0 a Premier League a Anfield.

Kwana uku tsakani wasan City da Liverpool, ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama za ta je Tottenham, domin buga Premier League.

A karawar farko a bana, Tottenham ce ta sharara 4-0 a ragar City, kuma a Etihad ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba.

Tun kafin nan Tottenham ce ta yi waje da City a Carabao Cup da cin 2-1 ranar Laraba 30 ga watan Oktoban 2024.

Wasa na shida da City za ta yi shi ne wanda za ta je Nottingham Forest a Premier League.

Forest ita ce ta ukun teburi da maki 47 da tazarar maki shida tsakani da City ta biyar ɗin teburi.

To sai dai City ta doke Forest 3-0 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar 4 ga watan Disambar 2024 a Etihad.

Wasa shida mai zafi da City za ta buga a jere:

Champions League Ranar Talata 11 ga watan Fabrairu

  • Man City da Real Madrid

Premier League Ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu

  • Man City da Newcastle

Champions League Ranar Laraba 19 ga watan Fabrairu

  • Real Madrid da Man City

Premier League Ranar Lahadi 23 ga watan Fabrairu

  • Man City da Liverpool

Premier League Ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu

  • Tottenham da Man City

Premier League Ranar Asabar 8 ga watan Maris

  • Nottm Forest da Man City