Da kyar idan Maguire zai buga wasan FA Cup da Man City

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mai tsaron bayan Manchester United, Harry Maguire na fatan zai murmure ya buga wasan karshe a FA Cup, bayan da ya ji rauni a wajen atisaye.

Likitocin kungiyar sun ce ɗan kwallon tawagar Ingila, zai iya yin jinyar mako uku kafin ya koma taka leda.

United za ta kara da Manchester City, mai rike da kofin bara a wasan karshe a FA Cup a Wembley ranar Asabar 25 ga watan Mayu.

Mai shekara 31 yana daga jerin masu tsaron bayan United dake jinya da suka hada da Raphael Varane da Victor Lindelof da Lisandro Martinez da Willy Kambwala da kuma Jonny Evans.

Maguire ya buga wasa tare da ɗan kasar Brazil, Casemiro a baya a fannin tsaron baya a United.

Sai dai ana cewa Evans zai iya buga wa United wasan da za ta je Crystal Palace, domin buga wasan mako na 36 a Premier, bayan da ya koma atisaye a makon jiya.