Arsenal na nazarin watsi da batun Sesko, United na zawarcin Kean

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na tunanin janye tayin fam miliyan 70 da ta gabatar kan ɗan wasan RB Leipzig Benjamin Sesko, mai shekara 22, sakamakon albashin da ɗan wasan na Slovenia ke buƙata, yayin da za ta iya karkata akalarta zuwa kan ɗan wasan Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27. (Mirror)

Manchester United na nuna sha'awarsta kan ɗan wasan Fiorentina da Italiya Moise Kean mai shekara 25, wanda ke da farashin fam 44.5m a ƙunshe a cikin kwantiraginsa. (La Gazzetta dello Sport)

Bayern Munich ta shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Chelsea Jamie Gittens, mai shekara 20. Zakarun na Jamus na da niyyar bai wa Borussia Dortmund fam miliyan 55 kan ɗan wasan. (Kicker)

Yunƙurin Juventus na sayen ɗan wasan gaban Manchester United Jadon Sancho mai shekaru 25 ya dogara ne kan ko ƙungiyar ta Italiya za ta ɗauki Francisco Conceicao daga Porto. (Corriere dello Sport)

Chelsea ba ta sanya Nicolas Jackson, mai shekara 24, a kasuwa ba, duk da sha'awar da ƙungiyoyin Saudiyya da na Turai ke nunawa kan ɗan wasan. (Sky Sports)

Liverpool ta amince ta sayar da ɗan wasan baya Jarell Quansah, mai shekara 22, ga Bayer Leverkusen kan farashin fam miliyan 35. (Fabrizio Romano)

Wrexham da Stockport County suna sha'awar tsohon ɗan wasan Wales da Rangers Tom Lawrence, mai shekara 31. (Sky Sports)

Ana sa ran ɗan wasan bayan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 29, zai bar Barcelona a bazarar nan. (Fabrizio Romano)