Abin da ya sa za mu soke rajistar kamfanoni 30,000 a Najeriya - CAC

Abin da ya sa za mu soke rajistar kamfanoni 30,000 a Najeriya - CAC
An wallafa

Hukumar da ke yi wa kamfanoni rijista a Najeriya ta Corporate Affairs Commission ta ce za ta rufe kamfanonin da ba su biyan kuɗin shekara-shekara.

Sabon shugaban hukumar ta CAC, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ya faɗa wa BBC Hausa cewa adadin kamfanonin da lamarin zai shafa ya kai 30,000.

A cewarsa, za su soke rajistar ne daga ranar 31 ga watan Disamba mai kamawa.

Kamfanoni da sana’o'in da matakin zai fi shafa su ne na shirya tafiye-tafiye, da ‘yan canji, da na haƙar ma’adanai da kuma lauyoyi.