Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Palace ta hana Man City hada maki uku a Etihad
Manchester City ta kara cin karo da koma baya, wadda ta tashi 2-2 a wasan Premier League da Crystal Palace ranar Asabar a Etihad.
Tun farko City ce ta fara cin kwallo biyu ta farko ta hannun Jack Grealish da kuma Rico Lewis daga baya Jean-Philippe Mateta ya zare daya saura minti 14 a tashi wasan.
Palace ta farke na biyu ne ta hanun Michael Olise a cikin minti na 95, wato bayan da lokaci ya cika aka yi kari.
Wannan shi ne karo na uku da City ta yi canjaras a jere a gida, hakan ya sa mai rike da kofin bara ta ci gaba da zama ta hudun teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Liverpool.
Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester United ranar Lahadi a wasan mako na 17 a Premier League a Etihad.
To sai dai Palace wasa daya ta ci daga 10 a baya, amma wannan sakamakon zai kara mata kwarin gwiwa a wasannin gaba da za ta fuskanta.
Ita kuwa City wasa daya ta yi nasara daga shida baya a lik, za kuma ta je Saudi Arabia domin buga Fifa Club World Cup ranar Talata.