Mai sayar da rake da masu murnar lashe zaɓe a cikin hotunan Afirka

An wallafa

Zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

Mai rake
Bayanan hoto, Wani mai sana'ar sayar da rake a birnin Kano da ke arewacin Najeriya ke gudanar da sana'arsa a ranar da ake kaɗa ƙuri'a, a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki na tarayya.
Wasu mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mata biyu ke ɗaga fure a lokacin wata zanga-zanga a Tunis babban birnin ƙasar Tunisiya ranar Asabar.
Miji da mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babban baƙo kenan da ya hallara a bikin buɗe gasar ƙwallon Circket da ake gudanarwa a birnin Pietermaritzburg na Afirka ta Kudu
Hoton yara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Can kuma a birnin Cape Town, masu kallo da dama ne suka taru domin, nuna goyon bayansu ga tawagar Afirka da Kudu a gasar ƙwallon Cricket ta duniya da ake gudanarwa.
sz

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Juma'a kuma mabiya addinin kirista a birnin Makoko sun yi addu'o'in neman zaman lafiya, kwana guda gabanin zaɓen Najeriya
M

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mutum ke kaɗa jita a lokacin da yake kan layin kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen Najeriya
Mutane

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mutane a birnin Legas ke nuna murnarsu bayan da aka bayyana sakamakon zaɓen rumfar da suka kaɗa ƙuri'a
mutum kwance a motarsa yana hutawa abinsa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwanaki biyu bayan zaɓen, a daidai lokacin da jam'iyyun adawa ke kiran a soke sakamakon zaɓen, wannan mutumin na kwance a motarsa yana hutawa abinsa
Masu tseren keke

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu tseren keke, a Rwanda, lokacin gasar tseren kekuna da aka gudanar a Kigali babban birnin ƙasar ranar Asabar - Henok Mulueberhane ɗan ƙasar Eritrea ne ya lashe gasar.