Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abun da ya sa kansar bakin mahaifa ke ci gaba da kashe mata
Abun da ya sa kansar bakin mahaifa ke ci gaba da kashe mata
An wallafa
Kimanin kashi 90 na mace-macen da sankarar mahaifa ta haifar sun faru ne a ƙasashe matalauta da masu matsakaicin tattalin ƙarfi.
Nahiyar Afrika kudu da hamadar sahara da tsakiyar nahiyar Amurka da kuma kudu maso gabacin Asia suna cikin yankunan da cutar ta fi addaba.
A kasashe 42 da ke fadin yankunan, cutar sankarar mahaifa ta fi kashe mata fiye da kowanne. Idan aka kwatanta da Switzerland, ita ce babban dalili na 19 inji kungiyar Medecins Sans Frontieres.
Mafi yawanci ana alakanta kamuwa da cutar da kwayoyin cutar papillomavirus.
HPV na saurin yaduwa ta hanyar haɗa jiki – musamman jima’i.