Za a bayyana gwarzon kwallon kafa na Fifa na 2022 ranar Litinin

Fifa Best Award

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Za a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2022 ranar Litinin da Fifa za ta karrama.

Cikin masu takara sun hada da Karim Benzema na Real Madrid da Lionel Messi da Kyalin Mbappe dukkansu daga Paris St Germain.

Benzema ya bayar da gudunmuwar da Real Madrid ta lashe La Liga da daukar Champions League na 14 jimilla a bara.

Ya ci kwallo 15 a Champions League, kuma shine kan gaba a sharara kwallaye a raga a La Liga a kakar da ta wuce.

Shi kuwa Mbappe, wanda PSG ta lashe Ligue 1 a bara da shi, ya ci kwallo 26 a wasa 46 da kuma yi wa tawagarsa ta Faransa zuwa gasar kofin duniya a Qatar..

Ya kuma taka rawar gani a gasar kofin duniya a Qatar da lashe takalmin zinare da cin uku a wasan karshe da Argentina ta lashe kofin a bugun fenariti.

Messi kyaftin din Argentina ya taka rawar gani a Paris St Germain tun bayan da ya koma Faransa da taka leda daga Barcelona a 2021.

Ya bayar da gudunmuawar da PSG ta lashe Ligue 1 a kakar farko da ya buga mata tamaula.

Shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya, shi aka bai wa fitatcen dan wasa a babbar gasar tamaula ta duniya ta 2022 a Qatar.

Fifa Award

Asalin hoton, Getty Images

Za a auna kwazon zakaran 2022 kan rawar da ya taka tsakanin 8 ga watan Agustan 2021 zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Za a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa a bikin da za a gudanar ranar 27 ga watan Fabrairun 2023 a hedikwatarta.

Za kuma a fara gudanar da bikin da karfe 9:00 daidai da agogon Najeriya da Nijar.

An tace ukun ne daga 14 da aka bayyana a baya, inda aka sa wasu kwararru suka tankade su zuwa ukun karshe da za a fidda gwani.

Kyaututtukan da za a lashe a kwazon 2022:

  • Fitatcen dan wasan kwallon kafa na duniya
  • Fitatciyar 'yar wasan kwallon kafa ta duniya
  • Mai tsaron ragar da ba kamarsa
  • Macen da ba kamarta a tsare raga
  • Fitatcen koci
  • Fitatciyar mai horar da tamaula
  • Kyautar Puskas Award
  • Kyautar wasa ba tare da gaba ba
  • Magoya baya mafiya da'a

Wadanda suka lashe kyautar 2021:

  • Fitatcen dan kwallon kafa na duniya: Robert Lewandowski
  • Fitatciyar 'yar wasa: Alexia Putellas
  • Gwarzon mai tsaron raga: Edouard Mendy
  • Gwarzuwar mai tsaron raga: Christiane Endler
  • Fitatcen koci: Thomas Tuchel
  • Fitacciyar mai horarwa: Emma Hayes
  • Kyautar Puskas Award: Erik Lamela
  • Wasa ba ttare da gaba ba: Tawagar Denmark da ma'aikaran lafiyarta
  • Fitattun magoya baya: Magoya bayan Denmark da na Finland