Matar da ta gina rijiyoyin ruwa fiye da 1000 a karkara

Matar da ta gina rijiyoyin ruwa fiye da 1000 a karkara
An wallafa

Hajiya Rabi’atu, wadda aka fi sani da Sarauniya, tana bi kauyuka tana gina rijiyoyi da burtsatse domin tabbatar da cewa mutanen garuruwan sun samu tsaftataccen ruwan sha.

Hajiya Rabi’atu ta ce ta samar da rijiyoyin ruwa da na burtsatse fiye da guda 1000 a fadin arewacin Najeriya ta hanyar gidauniyarta mai suna Sarauniya Charity Foundation.

"Abin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne lokacin da wasu Maguzawa suka nemi na gina musu rijiya guda za su Musulunta. Na gina musu guda biyar kuma sun Musulunta din. Har ma na gina musu masallaci," in ji ta.

Baya ga samar da ruwan sha da gidauniyar take yi, Hajiya Rabi’atu ta ce sun kuma tallafa wa marayu ta fannin karatu da tallafa wa zawara da sauran mata ta hanyar samun damar dogaro da kai.