Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 24/11/2024
Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 24/11/2024
An wallafa
A shirinmu na wannan makon Buhari Muhammad Fagge ya tattauna da abokin aiki Haruna Ibrahim Kakangi - wanda ya kai ziyarar aiki Amurka - kan abubuwan da ya gani a ƙasar musamman kan zaɓen shugaban ƙasar.
Haruna Ibrahim Kakangi ya bayyana abubuwan mamaki da ya gani a tsarin zaɓen Amurka, wadanda suka sha bamban da na ƙasashen nahiyar Afirka, irin su Najeriya da Ghana.
''Akwai bambance-bambance masu tarin yawa tsakanin Amurka da yadda ƙasashen Afikra ke gudanar da tarin zaɓensu,'' in ji Haruna Kakanki.