Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da ƙyar idan Maguire da Ugarte za su buga wasan Sociedad
Watakila Harry Maguire da Manuel Ugarte ba za su buga wa Manchester United wasa da Real Sociedad ba ranar Alhamis a Europa League.
Hakan ya biyo bayan da ƴan ƙwallon ba su yi atisaye ba ranar Laraba a shirye-shiryen da ƙungiyar ke yi na buga wasan farko zagayen ƴan 16 a Sifaniya.
Ƙungiyar da Ruben Amorin ke jan ragama na fatan komawa kan ganiya, bayan da Fulham ta yi waje da ita a FA Cup ranar Lahadi.
An cire United mai rike da FA Cup na bara a bugun fenariti a Old Trafford, bayan da suka tashi 1-1 har da ƙarin lokaci.
United na fama da ƴan wasan da ke jinya a shirin fuskantar Sociedad, sai ga Maguire da Ugarte sun shiga jerin masu jinya, bayan raunin da suka ji ranar Lahadi.
Ba a sa ran ƴan ƙwallon biyu za su je Sifaniya, kenan za su ci gaba da jinya tare da Amad Diallo da Kobbie Mainoo da kuma Lisandro Martinez.
Sauran da ke jinya a United sun haɗa da Luke Shaw da Jonny Evans da Mason da Altay Bayindir da Tom Heaton.
Matashi, Toby Collyer ya yi atisaye ranar Laraba ana sa ran za a je da shi Sifaniya, sai dai ba a yi wa matashi mai shekara 17, Chido Obi rigistar buga Europa League ba.
Ɗan wasan da United ta ɗauka a Janairu, Patrick Dorgu zai iya buga karawar, wanda aka dakatar wasa uku a gasar tamaula ta Ingila.