BBC ta gano yadda ake cin zarafi a gidan kula da tsofaffi na Kenya

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
BBC ta gano yadda ake cin zarafi a gidan kula da tsofaffi na Kenya
An wallafa

Gwamnatin Kenya ta ce za ta gudanar da cikakken bincike a gidajen kula da tsofaffi masu zaman kansu, bayan wani binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya bankado shaidun da ke nuna yadda ake cin zarafin tsofaffin a wani gidan kula da su a kusa da Nairobi.

Bidiyon da tawagar Africa Eye ta ɗauka a asirce, ya nuna yadda ma'aikatan gidan kula da tsofaffin ke duka da hantara da kyara da kuma ba su abinci a wulaƙance, har ma da watsi da kula da lafiyaru.

Sai dai mai kula da gidan ya musanta dukkan zargin da aka yi musu, inda ya ce ana bai wa tsofaffin da ba sa iya cin abinci da kansu kulawa ta musamman.

Sannan zargin rashin kula da lafiyarsu ma ba gaskiya ba ne.

Tsofaffin Kenya