Hukuncin mai ciki da mai shayarwa kan azumi
Hukuncin mai ciki da mai shayarwa kan azumi
An wallafa
Malama Habiba Alfadarai, ta yi bayani kan hukuncin addini game da rama azumi ko ciyarwa ga macen da take da ciki ko take shayarwa.
Malamar - wadda matar shehin malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Makari - ta ce malamai sun yi saɓani kan hukuncin mace mai shayarwa idan ta ajiye azumi.
Inda wasu malaman ke ganin za ta rama ne, wasu kuma suna ganin ba za ta rama ba, a maimakon haka za ta ciyar ne.
Dangane da matar da al'ada ta zo mata a cikin watan azumi kuwa, malama Habiba ta ce akwai ibadun da za ta iya gudanarwa



