Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBC ta gano yadda ake hana mata masu sanya gyale shiga wasu wurare a Masar
BBC ta gano yadda ake hana mata masu sanya gyale shiga wasu wurare a Masar
An wallafa
Sashen Larabci na BBC ya yi bad-da-kama domin gano yadda wasu 'yan kasuwa suke nuna bambanci ga matan da ke sanya mayafi ko gyale ko kuma hijabi a kasar Masar.
Kundin tsarin mulkin kasar ya haramta nuna wa mutane bambanci saboda launin fatarsu ko jinsu ko kuma matsayinsu a cikin al'umma.
Sai dai BBC ta gano wasu gidajen sayar da abinci da barasa da ba sa bari matan da ke sanye da mayafi ko gyale su shiga.