Yaya ƴan Najeriya suka karɓi shirin rage raɗaɗi na Tinubu?

Tinubu

Asalin hoton, Bola Tinubu?Twitter

    • Marubuci, Ahmad Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa

Ƴan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan shirin rage raɗaɗi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ƴan ƙasar da dama dai sun shiga cikin matsin rayuwa sakamakon janye tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya sanar a lokacin da yake karɓi rantsuwar kama aiki ƙarshen watan Mayu.

Baya ga cire tallafin man fetur, wani abu kuma da ya ƙara jefa ƴan Najeriya ƙuncin rayuwa shi ne na karyewar darajar naira.

A cikin jawabin talbijin da ya gabatar wa 'yan ƙasar ranar Litinin, Tinubu ya ce yana sane da halin tsadar rayuwa da ƴan ƙasar ke ciki, inda ya ce matakan da ya ɗauka su ne suka fi sauƙi, kuma da a ce akwai waɗanda suka fi su sauƙi, to da su zai ɗauka.

Cikin alƙawurran da Tinubu ya yi wa ƴan Najeriya na rage raɗaɗi a jawabinsa, sun haɗa da ƙara wa ma'aikata albashi da samar da aikin yi ta hanyar bai wa kamfanoni guda 75 rancen kuɗi naira biliyan ɗaya kowannensu a cikin wata tara.

Sauran alƙawurran akwai rabawa iyalai a jihohi 36 na fadin ƙasar tare da Abuja tan 200,000 na hatsi da kuma takin zamani da samar da motocin bas masu amfani da makamashin gas da kuma kashe biliyoyin kuɗi wajen noman shinkafa da masara da alkama da kuma rogo har kadada 400,000.

Tinubu ya ce daga lokacin da aka cire tallafin man fetur zuwa yanzu, gwamnati ta tara kuɗin da ya kai naira tiriliyan ɗaya a asusu.

Sai dai duk da irin ƙoƙari da kuma ɗaukar matakai da za su sauƙaƙa wa ƴan Najeriya da shugaban ya ce yana yi, ƙungiyar kwadagon ƙasar ta sha alwashin shiga zanga-zanga ta ƙasa baki-ɗaya a ranar Laraba.

Kungiyar ta ce cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi, gallazawa mutane ne wanda kuma ba za ta lamunta ba.

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun ce babu gudu ba ja da baya a wannan karo wajen shiga yajin aikin duk da yake a baya sun janye shi.

BBC ta duba abubuwan da 'yan Najeriya ke cewa game da irin matakan rage raɗaɗi da Shugaba Tinubu ya yi alƙawari.

.

Asalin hoton, Pst Clement/Facebook

Wani mai suna Akpevwe Clement ya yi tsokaci a shafin Facebook inda yake cewa "Najeriya na da manyan matsaloli guda biyu waɗanda su ya kamata a magance.

"Gwamnati ta gyara matatun man fetur, su dawo aiki yadda ya kamata, sannan na biyu kuma a shawo kan matsalar wutar lantarki, saboda tattalin arziki ba zai bunƙasa ba sai da wadataccen lantarki."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi ma a tsokacinsa kan jawabin da Shugaba Tinubu ya yi ranar Litinin, Sanata Shehu Sani ya yi bayani mai cike da raha inda ya kwatanta jawabin Tinubu da na magabacinsa Muhammadu Buhari.

Ya ce "Idan ka saurari jawabin Buhari, za ka buƙaci kofin shayi da zai sanya ka wartsake. Amma idan ka saurari jawabin Tinubu, za ka buƙaci fanka domin ka sha iska".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Sai kuma tsokacin da wata @caramel_flora ta yi a shafin Twitter, inda ta ce ko da shugaban ƙasa zai cire tallafi, sannan lita ɗaya ta koma 1,000, to fa hakan ba zai shafi manyan mutane ba, saboda tuni suka zama hamshaƙan masu kuɗi.

"Talakawa na shan wahala, ya kamata ka gane hakan shugaban ƙasa,".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Shi ma wani mai amfani da shafin na Twitter mai suna @TheoAbuAgada, ya faɗa wa shugaban ƙasa Tinubu cewa yanzu ba lokaci ne na yin jawabi ba, saboda ƴan Najeriya na cikin kunci, kuma ya kamata gwamnatinsa ta yi gaggawar shawo kan matsalar taɓarɓarewar tattali arziki.

"Idan ba za ka iya yin haka ba, to kamata ya yi kawai ka yi murabus."

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Malam Aliyu Saleh @AliyuSa25588107, wanda ya yi tsokaci a shafin BBC Hausa na Twitter, ya ce ƙarin albashi ba shi ne mafita ga al'ummar Najeriya ba, inda ya ce shawara ga gwamnati, ita ce kawai ta buɗe iyakokin ƙasar tare da bayar da damar shigar da abinci, saboda talaka ya samu sauƙin rayuwa.

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Shi ko Usman Isah @usmanisah02 ya ce me ya sa kullum talaka ke nuna yatsa ga shugaban ƙasa kawai, amma a manta da sauran jami'an gwamnati kamar gwamnoni da ƴan majalisar tarayya da na jihohi da ƴan kasuwa, waɗanda su ma ya ce sun taimaka wajen lalata kasa.

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 6

Sai kuma tsokacin Emu Kelvin @officialklev1 ya ce lokacin da ba a cire tallafin mai ba, tattalin arziƙin Najeriya na cikin yanayi mai kyau, sai da gwamnatin Tinubu ta shigo ne abubuwa suka ƙara lalacewa.

"Ba za ka cire tallafin man fetur ba sannan ka ƙara albashin ƴan majalisa, kuma ka ƙi ƙara mafi ƙarancin albashi".

Kauce wa X, 7
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 7

Muhammad Sameen @Muhdsameen14 ya ce Najeriya za ta gyaru da yardar Allah, amma ya ce sai kowa ya gyara mu'amalarsa da ɗabi'unsa saboda dukkan shugabanni da ake zaɓa cikin mutane suke.

.

Asalin hoton, Sani Mailangelange Yawuri/Facebook

Sai kuma tsokacin Sani Mai lange-lange Yawuri wanda ya ce ƙarin albashi abu ne da ya wajaba gwamnati ta yi, ganin halin matsin rayuwa da ƴan ƙasa ke ciki. Ya kuma ce su ma ƴan fansho da ƴan kasuwa ya kamata a dubi halin da suke ciki domin saukaƙa musu.

Kauce wa X, 8
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 8

Sai ra'ayin Ishaq Umar @IshaqUm36043260 wanda ya yi tambayar cewa wane mataki gwamnatin Tinubu za ta ɗauka don ganin tallafin da za ta bayar ya amfani talaka? saboda a cewarsa gwamnatin da ta gabata ma ta yi hakan, amma ba komai ne ya kai ga talaka ba.

Koma dai me ake ciki 'yan Najeriya cike da zaƙuwa suna dakon waɗannan shirye-shiryen rage raɗaɗi na Shugaba Tinubu don ganin irin tasirin da za su yi wajen kyautata rayuwarsu da kuma ciyar da ƙasar gaba.

Za kuma su ci gaba da fatan ganin hukumomi sun yi kyakkyawan amfani da kuɗaɗen da suke cewa an tara bayan cire tallafin man fetur wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa da manyan ababen more rayuwa.