Man City ta kammala cinikin Nunes daga Wolves

An wallafa

Manchester City ta cimma yarjejeniya da Wolves don sayen dan wasan tsakiya Matheus Nunes kan farashin fam miliyan 53.

Yarjejeniyar ta hada da batun bai wa Wolves 10% daga duk wata ribar da City ta samu kan dan wasan mai shekaru 25 a nan gaba.

Yanzu an bai wa Nunes izinin ya je a duba lafiyarsa a Manchester.

Wolves ta yi watsi da tayin da City ta yi mata a baya kan dan wasan na Portugal a makon da ya gabata, wanda ya kai kusan fam miliyan 60.

Nunes bai halarci atisaye ba kwanan nan bayan ya bayyana cewa yana son ya koma kungiyar wadda ke karkashin jagorancin Pep Guardiola.

Bugu da kari, Wolves ta amince da daukar dan wasan City na Ingila na kasa da shekara 21 Tommy Doyle a matsayin aro.

City ta so ta karfafa bangaren 'yan wasan tsakiyarta tun kafin Kevin de Bruyne ya samu rauni a kafarsa wanda zai iya sa ya yi jinyar watanni hudu.

Dan wasan West Ham Lucas Paqueta ya kasance zabin farko kafin a bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta Ingila na binciken dan wasan na kasar Brazil, mai shekara 25, kan yiwuwar keta ka'idojin yin caca.

Wolves ta dauko Nunes kan kwantiragin shekara biyar a bazarar da ta wuce, inda ta biya Sporting Lisbon fam miliyan 38.