Yadda aka yi na ci zaben fitar da gwani ina hannun ‘yan bindiga – Sadiq Ango Abdullahi

Yadda aka yi na ci zaben fitar da gwani ina hannun ‘yan bindiga – Sadiq Ango Abdullahi
An wallafa

Sadiq Ango Abdullahi na daya daga cikin mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga jirgin fasinja na Abuja zuwa Kaduna a watan Maris na 2022.

Kuma tun wancan lokacin Sadiq da sauran mata da yara suke hannun masu garkuwar har zuwa watan Satumba na shekarar ta 2022 bayan biyan kudaden fansa masu yawa.

Sai dai wani abu da ya faranta wa Sadiq rai shi ne yadda yana tsare a hannun ‘yan bindigar ya lashe zaben cikin gida na jam’iyyar PDP a takarar dan majlisar tarayya na mazabar Sabon Gari a jihar Kaduna.