Yadda mamayar Amurka ta tagayyara Iraqi

.

Asalin hoton, JEREMY BOWEN / BBC

An wallafa

Mamayar da aka yi a watan Maris ɗin 2003 ta zama babbar masifa ga Iraqi da mutanen ƙasar.

Ana sake samun hujjoji ne, idan aka auna yadda rayuwa ke taɓarɓarewa a ƙasar, da kuma zargin wani wawakeken kabarin mutane masu yawa da aka gano cikin sahara a wajen birnin Sinjar, wani yanki maras nisa da iyakar ƙasar da Syria.

Ɗaya daga cikin al’ummar da aka yi wa kaca-kaca a rikicin Iraƙi su ne mabiya addinin Yazidi, kuma suna tsaye suna kallon yadda ake kwashe ƙasar da ake haɗa tayels da ita.

A bayan wani shinge na waya a yankin, hoton wasu mutane ne masu yawa waɗanda mafi yawansu maza ne, da masu iƙirarin jihadi daga ƙungiyar IS suka kashe.

Mutanen ƙauyen Zile-Li ne da ke kusa da wajen haƙar, inda aka yi wa wasu mutane 1,800 kisan gilla a ranar 3 ga watan 2014.

Mabiya addinin Yazidi suna girmama littafin Qur’ani da Injila; addininsu kan samu tasiri daga duka addinan biyu.

Ƙungiyar IS na ɗaukar su a matsayin waɗanda ba su yi imani ba, don haka suka riƙa yi musu kisan ƙare dangi.

Hakan ya faru bayan Amurka da Burtaniya sun fice daga Iraqi a ƙarshen mamayarsu, wani abu da ya samar da alaƙa tsakanin kisan gillar da mamayar da aka yi musu, sannan wata shekara mai muni da ba za su manta da ita ba, ta biyo baya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cikin waɗanda suke kallon yadda ake kwashe ƙasar akwai Naif Jasso, wani babban malamin al’ummar Kocho ta mabiya addinin Yazidi da aka fi yi musu kisan gilla sama da Zile-li.

Ya ce a ƙauyen Kocho ‘yan ƙungiyar IS sun kashe mutum 517 cikin 1,250 da ake da su.

A ƙauyen Zile-li, an riƙa raba maza da matansu a wajen duba ababen hawa na masu ba da tsaro, sannan aka riƙa yi musu kisan gilla a wajen kwasar sinadarin haɗa tayels ɗin.

Sofian Saleh yana da shekara 16 a wancan lokacin, yana cikin mutanen da suka taru a wajen kwashe sanadarin da ake kashe mutane a ciki.

Yana ɗaya daga cikin mutane biyu kacal da suka tsira a ƙauyen Zile-li.

Yayin da yake jiran a kashe mahaifinsa da ɗan'uwansa da kuma wasu mutane su 30, sai kawai ya ga an kashe wasu mutane na daban.

An kuma tura gawawwakinsu cikin wannan ramin da ake haƙar sinadarin. Sannan aka ƙaraso kan ‘yan'uwansa.

“Sun ɗaure hannuwanmu ta baya, kafin su fara harbi. Suka ɗauke mu suka tura mu cikin wani rami” in ji shi.

An kashe mahaifin Sofian da ɗan'uwansa, amma shi ya tsallake rijiya da baya, saboda gawawwakin da suka danne shi lokacin da ake harbin.

.

Asalin hoton, CARA SWIFT/ BBC

IS na amfani da wata dabara da take kai musu.

Da farko sai su kashe duka mazajen da ke ƙauye, sannan su kwashe matan su bautar da su. Sukan ƙwace ƙananan yara daga hannun iyayensu mata, sannan su sanya su zama mambobin ƙungiyarsu, ƙarfi da yaji.

Wata mahaifiya da ke zaune a kusa da kabarin, ta yi tagumi tana share hawaye saboda tuna yadda aka ƙwace wani yaro daga hannunta aka bai wa masu iƙirarin jihadin.

A kusa da kewayen wayar wata mata ce mai suna Suad Daoud Chatto wadda ba ta fi shekara 20 ba, riƙe da wani hoto. Cikin fastar da take ɗauke da ita akwai hotunan wasu maza tara 'yan'uwanta, waɗanda duka su an kashe su, sai kuma hoton wasu mata biyu da suka yi ɓatan dabo.

Ta ce masu ikirarin jihadi sun kama ta a 2014 lokacin tana 'yar shekara 16, tare da wasu mata da kuma 'yan ƙanƙanan mata da aka tusa ƙeyarsu zuwa Syria. Inda ta zauna har 2019, lokacin da aka ceto ta, bayan ruguza daular da IS ta kafa.

.

Asalin hoton, CARA SWIFT/ BBC

“Mutane ne tamkar dabbobi, sun sanya wa mata ankwa a hannu tsawon lokaci. Har lokacin da muke cin abinci ba sa kunce mu,” in ji ta.

“Sun aura min maza da dama a lokuta da dama.... sun yi ta aurar matan da suka kwaso a matsayin bayi. Babu wanda suka bari.

Sun riƙa yi mana fyaɗe. Sun riƙa kashe mutane a kan idanunmu. Sun kashe duk mazan da ke bin addinin Yazidi – sun kashe ‘yan'uwan mahaifina takwas. Sun ga bayan iyalai masu yawa."

A ƙarshe dai wasu ‘yan jakunkuna ne muke iya gani na ƙasusuwan mutane a wurin. Akwai saura masu yawa da har yanzu ba a kwaso ba.

Lokacin da IS ta gama shiga Iraƙi a 2014, Amurka da Burtaniya sun kwashe nasu ya nasu sun fice daga ƙasar. Tunanin jihadi ya daɗe a yankin tun kafin a mamaye ƙasar, kuma harin 9/11 ya yi matuƙar ƙarfafa gwiwar masu iƙirarin jihadin.

Ba a kammala shafe tunanin jihadi da Osama Bin Laden ya kawo ba, da kuma masu tsattsauran ra’ayi, sai wani zamani na hargitsi da kashe-kashe a 2003, wanda ya tunzura masu iƙirarin jihadi suka riƙa tayar da hankaili.

Ƙawancen sojin Amurka da ƙabilu masu yawa sun kawo ƙarshen Al-Qaeda, sai dai hakan ya haifar da ƙungiyar IS wadda kuma ta fi waɗancan hatsari.

Iraƙi ta fi samun nutsuwa a bana fiye da a shekarun baya. An samu kwanciyar hankali a Bagadaza da birane irin su Mosul.

Amma har yau Iraƙi na ganin tasirin wannan mamaya a kullum. Hakan ya haifar da wani irin sauyi ga miliyoyin mutane, kuma ya canza fasalin ƙasar baki ɗaya.

Tsohon shugaban Iraƙi da ake yi wa kallon ɗan kama-karya Saddam Hussein – ya cancanci a kifar da gwamnatinsa – ya ɗaure mutane da dama ya kuma kashe dubban ‘yan Iraƙi.

Ya riƙa amfani da sinadarin guba mai kisa a kan ‘yan tawayen Kurdawa. Kawai matsalar ita ce yadda hakan ta faru. Yadda Amurka da Burtaniya suka sa kafa suka yi fatali da dokar ƙasashen duniya, da kuma rikicin da ya mamaye Iraƙi bayan gwamnatin Bush ta gaza cike gibin ikon da ta samar wanda hakan ya kawo sauyi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Na je New York kwanaki kaɗan, bayan kai wa tagwayen ginin cibiyar kasuwanci hari.

Wani gagarumin hari da aka kai wa dakarun Amurka, ƙasar da ta fi kowacce ƙarfin soji a duniya.

Kaɗuwar da hare-haren suka haifar, ta sa Shugaba George Bush faɗawa cikin yaƙi da ta’addanci a duniya, kan al-Qaeda da mambobinta da suke yawan tafiye-tafiye.

Firaministan Burtaniya Tony Blair ya miƙa wuya ta hanyar tsallaka tekun Atlantika domin kai nasa taimako.

Ya yi amannar cewa babbar hanyar da Burtaniya za ta iya taimaka wa White House ita ce kasancewa a tare da ita.

Cikin gaggawa suka cimma al-Qaeda a Afghanistan. Kafin ƙarshen shekarar, dakarun ƙawancen da Amurka ke jagoranta ta fatattaki Taliban daga iko, yayin da ta ƙi miƙa shugaban al-Qaeda, Osama Bin Laden.

A wannan lokacin Kabul babban birnin Afghanistan bai isa Amurka ba.

Shugaba Bush da masu ba shi shawara sun riƙa neman masu zama barazana ga Amurka a faɗin duniya. Sun riƙa zargin cewa ƙasashen da ba sa ga maciji da Amurka za su iya haɗa ƙawance mai hatsari da al-Qaeda.

Babbar ƙasar da suka riƙa zargi ita ce Iraƙi.

Amurka ta riƙa kallon Saddam Hussein a matsayin wata ƙaya, tun lokacin da ya aika dakarunsa cikin ƙasar Kuwait a 1990. Ba tare da wata hujja ba, ta ƙirƙiri wata alaƙa tsakanin ɓangarorin biyu.

A zahirin al’amari, shugaban Iraƙi ɗan kama-karya ne da bai damu da addini ba, hasali ma, yana yi wa masu tsattsauran ra’ayi barazana.

Mahaifin shugaban Amurka na lokacin HW Bush, ya yanke shawarar barin Saddam a kan iko bayan dakarun ƙawancen duniya da Amurka ta jagoranta sun kori dakarun mamaya na Iraƙin daga Kuwait a 1990.

Ina cikin Iraƙi lokacin da aka sanar da tsagaita wuta. Na yi amana sojoji ba za su amince da wannan kama-karyar ta ci gaba ba.

.

Asalin hoton, Getty Images

Shekara 12 bayan nan, a 2003 Amurka ta haɗa wani gangami mai ƙarfi don yin aikin da mahaifinsa ya ɗauke kai.

Yayin da Amurka da Burtaniya suka ga ba za su iya jiran kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yanke shawara a kan mamaya da kuma matakin soji ba, Bush da Blair sun yi iƙirarin cewa ba za a ba su damar mamayar ba.

Sai dai da dama ba su amince da wannan mamayar ba.

Cikin waɗanda ba su amince ba, akwai an BabbSakataren MDD na lokacin Kofi Annan, Wanda a wata hira da BBC wata 18 bayan mamayar ya ce wannan ba ya cikin daftarin MDD, a wani yaren kuma ya ce haramtacciyar mamaya ce.

Faransa da wasu mambobin ƙungiyar ƙawance ta Nato sun ƙi shiga cikin lamarin.

A gefe guda kuma, Tony Blair ya yi watsi da wata gagarumar zanga-zanga da aka riƙa yi a Burtaniya, kan shawararsa ta shiga wannan yaƙi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Amurka suna kayar da mutum mutumin Saddam a Bagadada

Babu mataki mai wuyar ɗauka a wajen duk wani shugaban ƙasa ko firaminista kamar matakin shiga yaƙi.

George Bush da Tony Blair sun shiga yaƙin gadan-gadan kuma sun kashe dubban mutane.

Hujjar da suka bayar a kan mamayar cikin gaggawa ta bayyana cewa, ba gaskiya ba ce.

Cikin gaggawa Amurka ta fara kai hare-hare da suka durƙusar da duniya, ƙasashe da dama sun suki matakin Bush, da cewa zai iya wargaza dimokraɗiyya da zaman lafiyar yankin, za kuma a iya samun kwararar makamai a yankin.

Amma Amurka, sai ta ce dakarunta ba kawai aminci za su samar ga ƙasar ba, har ma da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hakan kuma zai bai wa dimokradɗyya dama ta ratsa ƙasashen Syria da Iran da wasu na kusa da su.

Cikin ‘yan makonni suka hamɓarar da Saddam daga mulki

.

Asalin hoton, CARA SWIFT/BBC

A gefen wagegen kabarin nan da ke kusa da Sinjar, ɗan fafutukar kare 'yancin mabiya addinin Yazidi ya nemi kariya daga ƙasashen duniya.

Ya ce mayaƙan IS da suka yi kisan ƙare dangi a 2014, suna da karin harshe irin na ‘yan Iraƙi, wasu ma ‘yan Tel Afar ne, wani ƙauye da ke kusa da garinsu.

Farhad Barakat ɗan shekara 25, mai fafutukar kare 'yancin mutanen Yazidi ne da ya tsallake rijiya da baya, bayan tsallaka wani dutse a Sanjir. Ya ce har yanzu a tsorace suke da makwabtansu.

Ya ce makasan da ke zagaye da su, ƙabilu ne da kuma zuri’ar Larabawa masu makwabtaka. Ta yaya hakan zai yiwu?

Mutanen da suka kashe mu suka yi wa matan Yazidi fyade, ‘yan Iraƙi ne.”