Waiwaye: Naɗa sabon shugaban APC da kashe ƴanbindiga kusan 100 a jihar Neja

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Kamar kowane mako, wannan maƙala ta tattaro muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi.

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƴanbindiga fiye da 100 a jihar Neja

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Amry

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai waɗanda ake kira bijilanti sun samu nasara a wata fafatawa da suka yi da ƴan bindiga a ƙauyen Warari da ke Jihar Neja.

Rundunar ta ce a lokacin artabun da aka yi ranar Talata ta kashe fiye da 'yan bindiga 100 waɗanda ke gilmawa a kan babura.

Lamarin ya faru ne bayan da sojojin suka samu sahihan bayanai daga mazauna yankin game da hanyoyin da 'yan bindiga ke bi don satar shanu.

Wannan ne ya bai wa sojojin damar kitsa kwanton-ɓauna da ya kai ga fafatawar da ta kai ga hallaka ƴan bindigan da dama.

Jaridar PRNigeria ta ambato shaidun da suka ce sojojin sun yi amfani da motoci masu sulke da makamai na zamani wanda ya ba su galaba a kan 'yan bindigar.

Shugabannin al'umma a Warari sun tabbatar da girman rashin da 'yan bindigar suka tafka, inda suka bayyana cewa gawarwakin wasu daga cikin su sun bazu a tituna da gonaki da dazuka da ke kewaye da yankin.

Neja na cikin jihohin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

APC ta naɗa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugabanta

Nentawe Yilwatda

Asalin hoton, X/Nentawe Yilwatda

Kwamitin zartarwa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da nadin Farfesa Nentawe Yilwalda daga jihar Filato a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa.

An cimma matsayar ne yayin taron kwamitin zartarwar na kasa da ya gudana a Abuja.

Taron wanda ke gudana a fadar shugaban ƙasar, ya samu halartar Shugaba Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam'iyyar ta APC.

Akwai cikakken labarin a nan:

Rasuwar Sarkin Katsinan Gusau Ibrahim Bello

Marigayi Dr Ibrahim Bello

Asalin hoton, ZTSG

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rasuwar Sarkin Katsinan Gusau Dr Ibrahim Bello, wanda ya rasu ranar Juma'a yana da shekara 71 da haihuwa.

Sanarwar ta ce sarkin ya rasu ne a daren Juma'a 24 ga watan Yulin 2025 bayan doguwar jinya a wani asibiti da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Sanarwar da gwamnatin Zamfarar ta fitar ta ce: "Rasuwar mai martaba babban rashi ne ga jihar Zamfara da ma daukacin arewacin Najeriya".

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ne ya jagoranci jana'izar sarkin ranar Juma'a a Babban Masallacin Juma'a na Kanwuri da ke birnin Gusau.

Zanga-zangar 'yansanda a Abuja

Tsofaffin 'yansandan Najeriya

Ƴansanda da suka yi ritaya sun gudanar da zanga-zanga a Abuja babban birnin Najeriya kan yadda suka ce ana ba su abin da bai taka kara ya karya ba a matsayin fansho da kuma giratuti.

Tsoffin ƴansandan daga sassa daban-daban na Najeriya sun yi zanga-zangar ne ranar Litinin, kuma buƙatarsu ita ce a tsame su daga tsarin fansho na 'karo-karo."

"Idan da gaske ne tsarin na da kyau, me ya sa sufetan ƴansanda da mataimakansa da kwamishinonin ƴansanda ba sa ciki? In ji Iliyasu Aliyu, ɗaya daga cikin jagororin masu zanga-zangar.

Iyasu ya ƙara da cewa ya yi ritaya bayan kwashe shekara 35 yana bauta wa ƙasa amma a ƙarshe naira miliyan 2.5 kacal aka biya shi a matsayin giratuti, sannan ake ba shi naira 40,000 duk wata a matsayin fansho.

"Mene ne wannan kudin zai wa mutum?" In ji Ilyasu.

Ga cikakken labarin a nan:

Halin da Gwamnan Katsina Dikko Radda ya shiga bayan hatsarin mota

Dikko Radda

Asalin hoton, KTSG

A ranar Laraba ne aka sallami Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda daga asibiti bayan hatsarin motar da ya ritsa da shi.

Gwamnatin jihar Katsina ta ce lamarin ya faru ne a kan hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi 20 ga watan Yuli.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin X, ya nuna gwamna Radda na yin godiya ga jama'a bisa "addu'o'in da suke yi masa".

"Muna godiya da addu'o'i da ake ta yi mana. Allah ya jarabce mu da hatsarin mota amma mun samu sauki, muna nan a asibiti ana ci gaba da duba mu domin samun sauƙi," in ji gwamna Radda.

Bayanin da gwamnatin ta fitar game da hatsarin ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da gwamna Radda ke kan hanyarsa ta zuwa Daura, inda wata mota ƙirar Golf ta kauce hanyarta, kuma ta faɗa wa motar da gwamnan ke ciki.

Karanta cikakken labarin a nan:

Majalisa ta amince wa Tinubu ya ciyo bashi

Bola Tinubu

Asalin hoton, State House

A ranar Talata ne Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta ciyo bashin kuɗi daga ƙasashen waje da ya kai sama da dala biliyan 21 domin kashewa tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026.

Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan bashi daga cikin gida da waje, wanda shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wamakko, ya gabatar.

Akwai kuma shirin tara dala biliyan 2 daga cikin gida.

Tinubu ya ce za ayi amfani da bashin kuɗaɗen ne kan ɓangarorin gine-gine da noma da tsaro da wutar lantarki da fasahar sadarwa.

An ware dala biliyan 3 don farfaɗo da layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

Sanatoci da dama sun goyi bayan wannan shirin, inda suka ce hakan yana nuna adalci ga kowane yanki na ƙasar, kuma yana cikin tsarin da duniya ke bi wajen ci gaban tattalin arziki.

Komawar Sanata Natasha zaman Majalisar Dattawa

Natasha Akpoti

Asalin hoton, Natasha

A ranar Talata ne jami'an tsaro suka hana jerin gwanon motocin sanata Natasha Akpoti-Uduaghan shiga zauren majalisar tarayya, lamarin da ya sa ta sauka daga motarta ta taka ta shiga harabar majalisar tare da wasu magoya bayanta.

Sanatar wadda aka dakatar da ita na watanni shida ta yi niyyar komawa bakin aiki ranar Talata - bayan kotu ta umarci majalisar ta mayar da ita.

Sai dai lokacin da motarta ta isa majalisar, jami'an tsaro sun hana ta wucewa abin da ya janyo cecekuce yayin da magoya bayanta suka fara ihu suna ƙoƙarin kutsawa zuwa cikin majalisar.

Yunwa na ƙara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya sakamakon rikici

Yunwa

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda yunwa ke kara kamari a arewa maso gabas na Najeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda fiye da mutane miliyan 3.7 ke fuskantar matsananciyar rashin abinci.

A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa.

A Dikwa, manoma na tashi da safe su ratsa tafiya mai tsawo domin yin noma na 'yan awanni kafin su koma gida.

Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma, ya ce farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi, kuma kudin ɗinki da yake samu da dare bai isansu.

Modu Umar, wani shugaban al'umma, ya bayyana cewa yunwa tana haddasa cututtuka kamar gudawa a cikin yara da manya saboda rashin abinci da magani.

"Mutane na fita nesa su tara itace domin samun kudin siyan abinci." in ji shi.

ICRC dai ta ce ta fara wani shiri na taimakawa noma ta hanyar raba iri da kayan aikin noma ga sama da iyalai 21,000 a bana, domin tallafa musu a lokutan kaka da rani.